Dag MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Hajiya Asabe Nuhu, Shugabar kamfanin sarrafa kayayyakin amfanin gona da samar da abinci na kamfanin Northwest, ta yaba wa Mataimakin Shugaban ƙasa Alhaji Kashim Shettima wanda ya samu wakilcin Dr. Tofe Fashorye, da kuma Ministan tsaro na Nijeriya Alhaji Badaru Muhammad kan ziyarar da su kai wa kamfanin a matsayin ƙarfafa gwiwa a kamfanin da ma sauran kamfanoni da waɗannan shugabannin a matakin gwamnatin tarayya da kuma kwamishinan harkar kasuwanci Hon. Kibiya da sauran shugabannin kasuwar bajekolin Kano ƙarƙashin shugabancin Alhaji Garba Imam kan wannan ziyara a lokacin da aka buɗe bikin kasuwar bajekolin karo na 45 da cibiyar ciniki da masana’antu, ma’adanai da aikin gona, KACCIMA Kano, ta shirya a wannan lokaci da aka buɗe a ranar Asabar da ta gabata.
Haka kuma ta ce wannan ziyara ga kamfanin abin alfahari ne abun ƙarfafa gwiwa ne kuma ya na da kyau shugabanni su rinƙa irin wannan ziyara a kowane lokaci ga masana’antu, kamfanoni, ma’aikatu da sauran wurare na mu’amala ta cigaban ƙasa, inda ta ƙara da cewa wannan kamfani ya samar da aiki kuma ya na ba da aiki ga ɗimbin matasa waɗanda Allah kaɗai yasan waɗanda su ke cin abinci ta sanadin wannan kamfani da ke Dawakin Kudu a Jihar Kano.
A ƙarshe Alhaji Abbati Baƙo, ma’ajin KACCIMA, ya yaba wa shugabanni da suka halarci bikin bajekolin karo na 45 da kuma kamfanoni da shugabannin wannan hukumar bajekolin da ke Kano.
