Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
An bayyana ƙananan sana’o’ da harkar kasuwanci manya da ƙanana da mata suke yi da ma sauran al’umma a matsayin abu mai muhimmanci da ke kawo cigaban tattalin arziƙi a Nijeriya.
Saboda haka an an ƙarfafa cewa akwai buƙatar mata su dage da irin waɗannan sana’o’i wanda zai taimakawa kansu mazajensu, iyalansu, da ma sauran al’umma kamar dai yadda Hajiya Maryam Isah Jauro shugabar kamfanin INTISAR ta bayyana a wannan lokaci.
Haka kuma ta bayyana cewa ganin irin muhimmanci sana’o’in mata na dogaro da kai ya sa ta yanke shawara shekara da shekaru da suka gabata wajaen ganin, ta horar da mata sana’o’in zamani da na gargajiya a matsayin gudummawarta ga al’ummar Jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya.
Tun da farko ta yi kira ga mawadata da hukumomi da sauran ƙungiyoyi da ɗaiɗai kun al’umma kowa ya ba da gudummawa wajan yaƙar talauci da jahilci domin samar da al’umma da ƙasa ma alfahari da ‘ya’yanta kasancewar Nijeriya ƙasa ce mai albarka.
