Cibiyar NRI ta yi taron farko a Kano

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA KANO

Farfesa Clinton Brown da kuma Shugabar NRI ta Arewa, Esher Leonap ta Arewa, sun jagoranci taron ƙarfafa gwiwa da raba kyaututtuka ga ma’aikatansu da sauran masu mu’amala da wannan cibiya mai sarrafa kayayyakin abinci da itatuwa wajen samun magunguna da ke maganin cututtukan da suka damu al’ummar Nijeriya ba tare da an kai kuɗin wasu ƙasashe ba don siyo magani.

Wannan cibiya da ake kira NRI na taimakawa gaya wajen samar wa ɗimbin al’umma wajen dogaro da kai da bunƙasa tattalin arziƙi baya ga gudummawa a ɓangaren lafiya kamar dai yadda Farfesa Clinto Brown ya bayyana a taron da Nature’s Renaissance International LTD (NRI),  ta gabatar a ranar Lahadi a birnin Kano.

Ita kuwa, Esher Leonap, ya bawa mutanan Kano ta yi kan yadda su ke da ƙaunar baƙi da kyakkyawar mu’amala da mutane ba tare da nuna bambancin harshe ko ƙabila ba, tun da ga kan sarakunansu da shugabanninsu da, sauran al’umma musamman ganin yadda wannan taro ya samu wakilci daga fadar Sarkin Kano mai Martaba Malam Sunusi II.

Tun da farko sai da aka yi gwajin cututtuka da kuma ba da magunguna kyauta, inda kuma a ƙarshe aka raba kyaututtuka ɗaya daga cikin ma’aikatan NRI Hajiya Jamila ta samu kyautar mota sakamakon aikin ta ga wannan cibiya kamar dai yadda Hajiya Jamila ta bayyana.

Shi ma Mr. Abiodun Dare, da Mr. Eɓely James, sun bayyana gamsuwarsu da wannan taro na NRI karo na farko a Kano.    

By ukarofi