Uwargidan gwamnan Jihar Zamfara ta raba kayan kula da tsafta ga ɗaliban sakandire

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

A ci gaba da bikin ranar yaƙi da cin zarafin mata ta duniya ta bana, uwargidan gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal tare da haɗin gwiwa da cibiyar wayar da kan al’umma, a yau Juma’a ta bayar da tallafin kayayyakin kula da tsaftar muhalli guda 370 ga ɗaliban makarantar sakandaren mata ta gwamnati da ke Ƙaura Namoda.

Kayayyakin sun ƙunshi abubuwa masu mahimmanci kamar su pads, pomade, sabulun wanki, tufafi da littattafai da kayan motsa jiki da nufin haɓaka lafiya da tsafta a tsakanin ɗaliban.

A yayin rabon, Hurriyya Dauda Lawal ta jaddada mahimmancin tallafawa ɗalibai mata tare da ci gaba da ƙoƙarin wayar da kan jama’a domin yaƙar cin zarafin mata da ƙananan yara.

Ta tabbatar da wajibcin bunƙasa rayuwar al’umma musamman waɗanda a kaci zarafin su domin samun kwanciyar hankali da tallafawa tare da bada rahoton abubuwan da suka shafi cin zarafin mata.

“Ba zamu yarda da cin zarafin jinsi ba, kuma yana da mahimmanci a yi magana da neman taimako idan kai ko wani da ka sani ya fuskanci hakan,” in ji ta.

A halin da ake ciki a wata sanarwa da babbar mataimakiya ta musamman ga uwargidan gwamnan, Zara’u Musa ta ce uwargidan gwamnan ta bayar da tallafi ga dubban mata a unguwar Tudun Gandau da ke cikin garin Ƙaura Namoda ta hanyar raba shinkafa, kayan sawa, da tsabar kuɗi.

“Shirin wani ɓangare ne na kwanaki 16 na fafutukar yaƙi da cin zarafi da suka danganci jinsi”.

By ukarofi