Ƙudirin haraji: Talakawan Arewa ba su da shugabannin da za su tsaya musu – Gumi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmed Gumi, ya bayyana cewa yankin Arewa ba su da shugabanni kuma mutanen yankin sun zama tamkar marayu.

Sheikh Gumi yana wannan kalamai ne a yayin da yake bayyana ra’ayinsa game da ƙudurin sake fasalin haraji wanda ake cigaba da dambarwa a kansa.

Sheikh Gumi ya ce, “Arewa marayu ne, kullum nake cewa marayu ne. Mun kasa tsayar da shugaba ko kuma shugaba bai fito ba wanda zai rungumi kowa ya duba mashalar kowa. Ya duba talaka, ya duba mai arziƙi. Mun rasa.”

Sannan ya koka game da irin halin shugabannin Arewa suke nunawa, inda ya ce, “Kowa yana kukan gidansu ne….Kowa kansa da ‘ya’yansa shi ne kawai ya damu da shi. Har yanzu shugabanninmu haka suke a ƙasa irin wannan, sai dai mu ce la-haula-walaƙuwwata.”

Sai dai ya ce duk da haka, a ka da al’ummar Arewa su yanke tsammani da rahmar Allah.

“Amma kar mu yanke ƙauna da samun shugabanni da za su duba kowanen yanki,” in ji Sheikh Gumi.

Haka kuma ya yi magana game da irin illar da ke akwai game da ƙoƙarin yin shakulatin-ɓangaro da wasu ke yi da al’amuran Arewa ko ma fifita yankin Kudu.

Malamin addinin Musuluncin ya ce, “Tsirar da Arewa ba wai kawai tsirar da Arewa ba ne, tsirar da ƙasar ne Nijeriya gabaɗaya, domin idan Arewa ta lalacewa ta rikice ko Kudun ma ba za su samu zaman lafiya ba.”

A yayin da yake magana kan ‘yan Arewa da halin talakawanta, Sheikh Gumi ya ce kamata ya yi mutanen Arewa su mai da hanakalinsu “wajen haɗa kanmu mu yi abin da ya kamata kuma komai za mu yi mu yi shi da ilimi. Mu mutane ne masu ‘atifa’, wato mutane masu yanke hukunci da abin da suke so.”

Sai dai ya nuna takaicinsa game da yadda a baya aka yi ta kira wajen zaɓen shugabannin da suka dace, inda yake cewa;

“Tun tuni mun gaya muku ga irin shugabannin da ya kamata su rungume mu, kuka ce a’a ga wanda kuke so. Ba ku duba kwaliti na shugabancin da ake so ba. Wasu ma an ce a roƙi Allah ya zaɓa mana shugaban da muke so, sai ka ji an ce ka ji munafiki, wanda ya ce a yi abin da Allah ya ce, sai ace ka ji munafiki. To ga shi nan yanzu mun gani. Allah ya shiryar da mu.”

Da yake magana game da ƙudirin sake fasalin haraji, Sheikh Gumi ya ce, tsarin harajin da ake amfani da shi yanzu ya fi wanda aka kawo haɗari.

Don haka yunƙurin da shugaban ƙasa ya yi abu ne mai kyau, amma akwai abubuwa da ya kamata a lura da su dangane da ƙudurorin.

Sheikh gumi ya ce akwai batun kallon halascin wani ɓangare na kuɗin harajin da ake magana a kai, “akwai kuɗin giya.

Kamfanonin har da masu yin giya kuma mun san cewa Annabi (S.A.W) ya ce, an la’anci mai shan kuɗin giya.”

Shehin malamai ya ce, akwai kuɗin giya a cikin kuɗin don haka ya buƙaci a tsari da zai keɓance jihohin Arewa 12 da suka yarda da shari’ar addinin Musulunci ita ce shari’arsu.

Hakazalika, Sheikh Gumi ya yi jan hakali game da kuɗin caca inda ya buga misali da ‘bet Naija’ da makamantansu, “kada a sa musu (jihohin) duk nau’in kuɗin abin da shari’ar Musulunci ba ta yadda da shi ba, domin bai halatta mu riƙa cin haramun mu ɗauka Allah zai taimake mu.”

Sheikh Gumi ya ce akwai buƙatar a sauƙaƙa wa kansa ta fuskar abubuwa na ma’adanai da ake samunsu daga ƙarƙashin ƙasa kamar mai da iskar gas inda ya ba da misali da Hadisin Manzon Allah (S.A.W) da cewa, “mutane suna tarayya a kan abubuwa guda uku: ciyawa da ruwa da kuma wuta.”

Gumi ya ce man fetur wuta ne da ake amfani da shi a mota kuma ya kamata, “mutane su zamo suna da daidaito a cikin al’amarinsu. Ya zama ƙasa mai, mai kowa ya wadata da shi.”

Haka kuma ya ce canja dokar na da kyau, “a cikin kundin dokar akwai abubuwa masu kyau waɗanda ba za a yi inkari ba. A ciki akwai batun cire wa talakawa haraji. Kamar yadda na karanta, duk wanda albashinsa yake ƙasa da 800,000 a shekara, za cire masa haraji.”

Sai dai ya ce, ya kamata a ƙara albashin sama da 800,000 kuma cire harajin shi ne albarka domin haraji musiba ce a kan al’umma. Inda ya buga mmisali da cewa a ƙasashen da aka cigaba idan al’umma na fama da talauci kamar yadda ake fama da shi a Najeriya, ana cire wa talakawan ne haraji tare da rage kuɗin ruwa da ake ɗorawa kuɗin rance da ake ba wa al’umma don mutane su samu damar karɓar rance wajen yin aikin noma da sauran ayyuka da za su haɓaka tattalin arziƙin ƙasa.

Hakazalika, Sheikh Gumi ya ce, akwai harajin marar kyau da ake yi yanzu idan mutum zai tura Naira 10,000, sai a ce sai an ɗaukar wa mutum Naira 50.

“Wannan za su kawo wa rayuwar mutane cikas.”

Sannan ya soki batun jibga wa al’umma haraji daban-daban kamar harajin gwamnatin tarayya da na jiha da na ƙananan hukumomi duk a kan mutum ɗaya wanda ya ce hakan zalunci ne.

Ya ce, maishe da haraji baiɗaya abu ne mai kyau gaske da wannan ƙuduri ya kawo don haka ya ce, “a yi gyaran yana da muhimmanci, amma a zauna a haka cuta ce. Don haka yunƙurin ma ace za a yi gyaran babban alheri ne.”

Daga ƙarshe ya ba da shawara kan a gayyaci masana domin su duba wanna kundi kuma a duba kowanne yanki a yi masa abin da ya dace da shi.

By ukarofi