


Daga BELLO A. BABAJI
A safiyar ranar Juma’a ne jami’an tsaro a Kano suka tare mashigar Fadar Sarki ta Gidan Rumfa tare da dakatar da Sarki Muhammadu Sanusi zuwa taron Sarauta a Bichi.
Wata majiya daga Masarautar Kano ta ce an tsara cewa Sarki Sanusi zai halarci taron gabatarwa na sabon Wamban Kano, Munir Sanusi.
Saidai ana gaf da tafiya taron ne, jami’an tsaron suka cika Masarautar tare da faɗa wa Sarkin cewa ya cigaba da zama a Fadar ba tare da wani cikakken bayani ba.
Majiyar ta kuma an cika sauran ƙofofin shiga Masarautar da motocin jami’an tsaro ta yadda Sarkin ba zai samu damar ficewa ba.
Haka kuma wata majiya ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar ya aika da wata tawaga wadda ita ma jami’an tsaron sun ƙi amincewa ta shiga cikin Fadar.
Jaridar ‘News Point Nigeria’ ta ruwaito cewa ita ma Masarautar Bichi wadda ke da nisan kilomita 50 daga ta Kano, jami’an tsaro sun yi dandanzo tare da toshe mashigar ta.
Jami’an tsaron sun haɗa da ƴan sanda da sojoji da DSS.
A baya ne Majalisar Dokokin jihar ta amince da ƙudirin dokar masarauta wanda ke neman a rushe masarautu biyar da tsohuwar gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta samar.
Masarautun sun haɗa da na Bichi, Rano, Gaya da kuma na Ƙaraye.
