
Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse
Kimanin gurabe 2,922 ne Hukumar Samar da Aikin yi ta ƙasa (NDE) ta ware wa Jihar jigawa domin bai wa matasa horo akan sana’ar kiwon awaki da kaji da kifi da da kuma waɗanda za a koyawa gyaran mota da aikin sola a ƙoƙarin gwamnatin Tarayya na magance zaman banza a tsakanin matasan ƙasar nan.
Hakan na daga cikin shirin hukumar a ƙoƙarinta na samawa matasa madogara tarevda haɗin-gwiwar Hukumar Jin-daɗin Mata da walwalar Jama’a ta ƙasa da aka shirya domin a sauya rayuwar al’umma daga mawuyacin halin ƙunci da matasa suke ciki.
A kwanan baya ne hukumar ta yi shelar cewar duk matashin da yake da buƙatar shiga bitar da ya cike takardun neman gurbi ta layukan da ta ware domin koyon sana’oin da ya ke buƙata a ƙarƙashinta.
Da ya ke jawabi a lokacin buɗe bitar, jami’in shirin na shiyyar Jigawa, Malam Hamza Muhammed wanda shine ya wakilci shugaban NDE, Mista Silas A. Agara, ya ce hukumar ta ware guraben mutum 93,731 da za a koya wa sana’ar a faɗin Nijeriya gaba ɗaya da nufin samawa matasa aikin yi .
Ya kara da cewa an ware za a dauki Matasa goma daga kowacce mazaɓar ta siyasa a faɗin Nijeriya da adadin mazaɓun ya kai 8,809 da ake da su a Nijeriya.
Ya cigaba da cewa a ƙarƙashin shirin akwai sana’o’i guda 30 da aka ware za a gwadawa matasan.
Ya kuma ce a ƙarshen bitar da aka shirya wa matasan a Dutse, za a bai wa dukkan matasan jari da kayan sana’ar da suka koya domin su zamo masu dogaro da kawunansu anan gaba.
