Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun ta cafke wasu mutane huɗu bisa zargin sace gawar manomi mai suna Joel Omirenya, a ɗakin ajiye gawa na Asibitin Sacred Heart da ke unguwar Lantoro a Abeokuta.
A cewar rahotanni, Omirenya ya kamu da rashin lafiya ne inda aka garzaya da shi asibiti domin yi masa magani cikin gaggawa, amma ya mutu a lokacin da ake kwantar da shi kuma aka ajiye gawarsa a ɗakin ajiye gawa na asibitin.
Da yak e magana kan lamarin, ɗan Omirenya ya ce, ’yan uwa sun kammala shirin kai gawar mahaifinsa zuwa garinsu na jihar Benuwai a lokacin da ƙoƙarin gano gawar tasa a ɗakin ajiyar gawarwaki ya ci tura.
Ya kuma bayyana cewa, an miƙa ma’aikacin ɗakin ajiye gawarwakin mai suna John Olaade ga ’yan sanda a ofishin ’yan sanda na Adatan kuma an sanar da ’yan uwansa gawar da ta ɓata.
Ya ce, “A ranar 13 ga Fabrairu, 2023, da mahaifina ya yi rashin lafiya, muka garzaya da shi Asibitin Zuciya na Lantoro da ke Abeokuta, aka kwantar da shi. Bayan an kwantar da shi mako guda, ya rasu kuma muka yanke shawarar ajiye shi a ɗakin ajiyar gawa na asibiti. Mun biya Naira 25,000 don yi wa gawarsa sutura da gyaran fuska.
“An ce mana Naira 25,000 za ta yi kwana biyar, sannan za a riƙa kula da gawar da ke ɗakin ajiye gawarwaki Naira 1,000 a kowace rana, muka amince, muka biya, aka ba ni takardar da zan riƙa gabatarwa duk lokacin da na zo duba gawar.
“Bayan mako guda, na dawo ɗakin ajiyar gawar don duba gawar kuma tana nan. Na kuma koma a ranar 15 ga Maris inda na tarar tana nan. Amma a ranar Juma’a, 21 ga Maris, 2023, na kira ma’aikacin gawarwakin, John Olaade, cewa a shirye muke mu kai gawar garinmu a Jihar Binuwai kuma za mu kawo tufafi da sauran abubuwan da za su yi wa gawar sutura a ranar Lahadi, don haka za mu iya karɓa da sassafe ranar Litinin.
“Lokacin da muka isa ɗakin ajiyar gawarwaki ranar Lahadi, ya buƙaci mu biya maƙudan kuɗi na asibitin sannan ya umarce mu da mu biya kuɗin da mamacin ya sanya a asusun ajiyarsa na banki. Na biya Naira 51,000 bayan na biya sai na buƙaci in ga gawar kafin ya fara yi mata sutura kuma da ya shigar da mu ɗakin ajiyar gawarwaki, ba mu sami gawar mahaifina a wurin da aka ajiye ta ba.
“Na tambayi abin da ya faru sai ya fara kame-kame yana neman gawar mahaifina. Na kuma taimaka wajen binciken da aka fara da misalin ƙarfe 4 na yamma har zuwa ƙarfe 7 na yamma amma ba mu iya gano gawar tana ina ne ba, sannan kuma mun kashe Naira 140,000 don ɗaukar motar ɗaukar marasa lafiya domin kai gawar garinmu.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, inda ya ce an kama wasu mutane huɗu da ake zargi.
