Gwamnatin Tarayya na bincikar GTBank, MTN da Air Peace akan koke-koken kwastomomi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Haƙƙin Masu Saye da Amfani da Kayayyaki a Nijeriya (FCCPC) ta ƙaddamar da wani babban bincike kan ƙorafe-ƙorafen masu al’umma a kan wasu bankuna, da kamfanonin sadarwa da wasu kamfanonin sufurin jiragen sama.

Daraktan hulɗa da kamfanoni na FCCPC, Ondaje Ijagwu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

A cewar Ijagwu, binciken da za a fara a ranakun 3, 4, da 5 ga watan Disamba, an yi shi ne domin magance matsalolin rashin mutunta haƙƙin abokan ciniki da cin hanci da rashawa.

A ɓangaren banki kuwa, FCCPC ta ce za ta binciki bankin Guaranty Trust (GTB) bisa rahotannin gazawar hanyar sadarwar da ke hana kwastomomi samun kuɗaɗensu ko amfani da aikace-aikacen banki.

A ɓangaren sadarwa, kamfanin MTN na Nijeriya na fuskantar bincike dangane da ci gaba da ƙorafe-ƙorafe daga jama’a kan ayyukansu, da ƙarancin bayanan da ba a bayyana ba, da kuma rashin isasshen kulawa da abokan ciniki.

Hakazalika, kamfanin na Air Peace Limited zai magance zarge-zargen cin gajiyar farashin tikitin, da suka haɗa da ƙarin farashin tikitin shiga gaba a kan wasu hanyoyin cikin gida.

Hukumar ta bayyana cewa, ana gudanar da waɗannan bincike ne a ƙarƙashin dokar kare haƙƙin cinikayya da masu amfani da kayayyaki ta tarayya (FCCPA) 2018, musamman sashe na 17, 18, 32, 33, 80, 110, 111, 112, da 113, wanda ya baiwa hukumar FCCPC damar gudanar da bincike don warware ayyukan da ke lalata haƙƙin jama’a, rushe kasuwanni, ko haifar da gasa mara adalci.

Ya ƙara da cewa, haɗin gwiwa tare da waɗannan kamfanoni zai ba da damar magance matsaloli, fayyace ayyukan kasuwanci, da tilasta bin ƙa’idodi da tsari.

Za a buƙaci kamfanonin da su bayyana a gaban Hukumar a ranakun da aka keɓe don bayar da bayanai da martani don bai wa Hukumar damar yanke shawara da warware matsalolin da ke kan gaba cikin gaggawa.

By ukarofi