FAZAMS ta yaba wa Gwamna Dauda kan farfaɗo da harkar Ilimi a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Ƙungiyar daliban Zamfara ta FAZAMS, ta yaba wa gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal kan inganta fannin ilimi a jihar.

Shugaban ƙungiyar mai barin gado, Kwamared Abubukar Galadima ya bayyana hakan a wani taron ƙungiyar da manema labarai wanda aka gudanar a Hedikwatar hukumar ilimin bai ɗaya ta jihar.

A cewarsa, yabon ya zama dole duba da yadda gwamnan ya ayyana dokar ta-ɓaci akan ilimi wanda ya haifar da kyakkyawan sakamako na kawo sauyi a fannin cikin shekara ɗaya da rabi.

Kwamared Galadima ya ce, taken taron shi ne ‘Gina nasarorin da aka samu, da share fagen jagoranci sabbin shuwagabanni a nan gaba’.

Ya kuma ce ƙungiyar a lokacin shugabancinsa ta samu nasarori kamar haka, samar da JAMB ga ɗalibai 15 na Sakandare, shirin wayar da kan al’umma na JAMB, ga ɗaliban Sakandare 115, inda ta bayar da tallafin kayan rubutu ga ɗalibai 500.

Sauran nasarorin sun haɗa da biyan kuɗaɗen karatu na zangon 2023/2024 a makarantu 150, tallafin karatu na ci gaba ga ɗaliban makarantun sakandare 1,050, kammala ba da tallafin karatu ga ɗaliban 1,449, ba da izinin kulawa ga ɗaliban ƙasashen waje 34, Rarraba Kayan Abinci ga dalibai 637 da sauran su.

“A jimillance kimanin Ɗalibai 3,948 ne suka amfana a cikin watanni 12 a jere na jagorancin yin karatu cikin sauki a jihar.”

Kwamared Galadima ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta ƙara jajircewa wajen magance ƙalubalen da ɗaliban ke fuskanta domin kammala karatunsu cikin sauki.

Ya yaba wa uwar gidan gwamnan, Hajiya Hurriyya Dauda Lawal da hukumar bayar da tallafin karatu ta jiha (UBEC) da ofishin sakataren gwamnatin jihar bisa goyon bayan da suke bai wa ƙungiyar a ƙarƙashin jagorancinsa har suka cimma burin da aka sanya a gaba.

By Babaji