Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Wani jigo a ƙaramar hukumar Maradun ta Jihar Zamfara, Kwamared Haliru Attahiru ya koka kan kalaman da gwamna Dauda Lawal na jihar yayi kan sace mutane 50 da aka yi kwanan nan, inda gwamnan ya fito tana mai cewar hakan bai faru ba.
A baya dai gwamnan ya ƙaryata rahotannin garkuwa da mutanen Ƙauyen Kakindawa da wasu ‘yan bindiga suka yi a Ƙauyen da ke ƙarƙashin gundumar Gidan Goga a ƙaramar hukumar Maradun da wasu kafafen yaɗa labarai su ka yi.
Attahiru a wata hira da manema labarai ya bayyana cewa kamata ya yi gwamna Dauda ya yi bincike ta hannun shugaban ƙaramar hukumar ko kansiloli ko kuma sarakunan yankin kafin ya ƙaryata labarin.
Ya ƙara da cewa “Abin takaici ne matuka ga Gwamna ya ƙaryata abin da bai bincika yadda abun yake ba don samun haƙiƙanin abin da ya faru a yankin.”
Ya ci gaba da cewa, mazauna yankin sun kasance masu bin doka da oda, yana mai jaddada cewar babu yadda za ayi su yaɗa ƙarya domin ɓata sunan gwamnati.
Attahiru ya bayyana cewa, mutanen Gidan Goga da ƙauyukan na fuskantar hare-haren ‘yan bindiga akai-akai, inda har yanzu mutane da dama na hannun ‘yan bindigar.
Ya ƙalubalanci Gwamna Dauda Lawal da ya binciki lamarin da ya faru kwanan nan inda aka yi garkuwa da mutane 50.
“Don wane dalili ne mutanen Kakindawa za su ƙirƙiro satar mutanen kuma mun san cewa gwamnatin jihar ba ta bayar da tallafin kuɗi ko kayan abinci ga waɗanda abin ya shafa, don haka me yasa muka gayawa duniya halin da muke ciki,” inji shi.
Attahir ya buƙaci Gwamna Lawal da ya janye kalamansa, ya fuskanci matsalar rashin tsaro da komai, inda ya koka da cewa, “Rufewa ba zai taɓa magance matsalar ‘yan fashi a jihar ba.
