Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Masu sana’ar hada-hadar kuɗi ta POS sun zama sanannu a duk faɗin Nijeriya, inda suke amfani da na’urar cirar kuɗi wajen samar da kuɗaɗe cikin sauƙi ga miliyoyin mutane ba tare da samun damar zuwa banki ba, musamman a yankunan karkara da ke da wuyar samun banki.
Mazauna birane da ƙauyukan Nijeriya, a ‘yan makonnin nan suna kokawa kan ƙarancin takardun kuɗi a na’urorin cirar kuɗi na ATM da wuraraen masu sana’ar aikawa da cire kuɗi ta POS, wani abu da ke ƙara haifar da fargaba a zukatan al’umma.
Masu sana’ar ta POS na kokawa kan yadda suka ce ba su samun kuɗaɗe da yawa a bankunan idan suka je cira, saɓanin yadda suka saba samu a baya.
Wannan ne ma dalilin da ya sa wasu masu sana’ar a Abuja suka haƙura da ita ko suka rufe saboda rashin garin kuɗin.
Sannan ga wazanda ake samun kuɗin a wajensu, ba a samu da yawa, sannan kuma sun ƙara yawan kuɗin da suke cazar mutane.
A wasu sassan Abuja, masu sana’ar na karɓar naira 400 kan kowace naira 10,000, saboda yadda suka ce suna shan wahala wajen samo kuɗaɗen.
Wata mai sana’ar POS a Abuja mai suna Esther Nwanna, ta shaida wa manema labarai cewa yanzu kullum sai ta je bankuna aaalla biyar da take hulɗa da su kafin ta iya samun 100,000 da za ta fito wajen sana’ar tata da safe.
”Da safen nan sai da na je bankuna biyar, kuma dukkansu ba a kusa da juna suke ba, amma wallahi da kyar na samo naira N100,000 da zan fito in fara da ita”, a cewarta.
Shi ma Abubakar Jibril mai irin wannan sana’a, ya ce sai da ya je bankuna huɗu kafin ya samo N70,000.
”Bankunan da na je ba a kusa da juna suke ba, dole sai na hau abin hawa zuwa kowanne, sannan na dawo wurin sana’ar tawa. Ka ga ai dole na ƙara kuɗi ni ma in dai ina so in ci gaba da sana’ar,” a cewarsa.
”A baya banki guda nake zuwa kuma ko nawa nake so za su ba ni domin gudanar da harkokina, amma yanzu abubuwa sun sauya, bankin ma babu kuɗaɗen balle su ba mu.”
Wani ma’aikacin banki wamda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce abin da ke faruwa shi ne ana tattara tsofaffin takardun kuɗi ne a wani ɓangare na shirye-shiryen daina amfani da su.
”Idan ba ka manta ba, a lokacin gwamnatin tsohon Shugaba ƙasa Muhammadu Buhari an sauya fasalin wasu takardun kuɗin ƙasar, kuma aka saka wa’adin daina amfani da su, amma saboda ƙarar da wasu gwamnoni suka shigar aka ɗaga zuwa wani lokaci na gaba”, inji shi.
A shekakar 2022 ne Muhammadu Buhari ya ba da umarnin sauya fasalin takardun kuɗi na N1,000 da N500 da kuma N200, tare da saka wa’adin daina amfani da tsoffin zuwa ƙarshen shekarar 2022.
Sai dai bayan wasu gwamnonin ƙasar sun garzaya kotun ƙolin ƙasar don ƙalaubalantar taƙaitaccen lokacin da aka bayar na daina amfani da tsoffin takardun kuɗin, kotun ta bayar da umarnin cigaba da amfani da su har zuwa shekara guda, inda daga baya ta yi hukuncin cewa a ci gaba da amfani da su ba tare da iyakance lokaci ba.
Ma’aikacin bankin ya kuma ce wani ƙarin dalilin shi ne rage yawan kuɗin da ke yawo a hannun mutane, wanda ke ɗaya daga cikin tsare-tsaren gwamnati kan tattalin arziki.
A cewarsa, ”Ya kamata a ce kuɗaɗen nan a banki suke, don haka wannan ma na daga cikin dalilan ƙarancin kuɗin da ake gani yanzu.”
Don haka ne ya ce idan an shigar da tsoffin takardun kuɗi banki, ba lallai ne ma a buga adadin kuɗin da ya kai su yawa ba.
”Misali idan an shigar da naira biliyan ɗaya banki na tsoffin takardun kuɗi, to ba za a ce dole sai an buga naira biliyan ɗaya na sabbin kuɗi ba, a maimakon haka za a rage adadin da za a buga domin su zagaya a hannun mutane,” a cewarsa.
Ya ƙara da cewa, wannan su ne manyan abubuwan da suka janyo ƙarancin garin kuɗi a tsakanin al’umma.
