HOTUNA: Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Ghana mai jiran gado ya ziyarci Tinubu a Abuja

Spread the love

Shugaban Ghana mai jiran gado, John Dramani Mahama, ya kai ziyara ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa. Wannan ziyara ta samu tabbaci ne ta hannun mataimakin shugaba Tinubu na musamman kan kafofin sada zumunta, Dada Olusegun, wanda ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata.

A cewarsa, “Shugaban Ghana mai jiran gado, H.E John Dramani Mahama, ya kai ziyara ta girmamawa ga Shugaba Tinubu a fadarsa, Villa ta Ƙasa, jiya.” Wannan ziyara ta biyo bayan saƙon taya murna da Shugaba Tinubu ya aike wa Mahama bayan nasarar da ya samu a zaɓen Ghana da aka gudanar ranar 7 ga Disamba.

A baya dai, Shugaba Tinubu yayin wata tattaunawa ta waya da Mahama, ya bayyana fatan cewa dawowarsa kan mulki zai inganta zaman lafiya da tsaro a cikin ƙungiyar tattalin arzikin yammacin Afirka (ECOWAS). Tinubu ya kuma nuna shirin yin aiki tare da gwamnatin Mahama domin ƙarfafa dangantakar kasashen biyu a fannoni daban-daban.

John Mahama ya riƙe muƙamin mataimakin shugaban Ƙasar Ghana daga 2009 zuwa 2012, ya kasance ɗan Majalisa daga 1997 zuwa 2009, tare da riƙe muƙaman minista da na mataimaki tsakanin 1998 zuwa 2001.

By ukarofi