Wajibi ne a kula da damuwar mutane kan ƙudirin gyaran haraji – Shekarau

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma shugaban ƙungiyar ƴan demokraɗiyya ta Arewa (LND), Sanata Ibrahim Shekarau ya nuna muhimmancin kulawa da damuwar al’umma kan ƙudirin dokar gyaran haraji da Shugaba Tinubu ya gabatar wa majalisa.

Shekarau ya bayyana hakan ne cikin rahoton kwamitin ƙungiyar game da ƙudirin wanda a yanzu ya ke hali na tantance wa a majalisa.

Lamarin ƙudirin harajin ya haifar da cecekuce acikin al’umma musamman gwamnoni da wasu manyan Arewa waɗanda ke neman a sake nazari game da shi.

Makonni biyu da suka gabata ne LND ta samar da kwamiti da zai yi nazari game da ƙudirin don bayyana matsayarta a kai.

Ƙungiyar ta gano cewa ƙudirin zai taimaka wajen ɗorewa ga tattali arziƙi, yayin da ta ke ƙoƙarin warware matsalolin doka da al’adu da kuma shugabanci.

A lokacin da ya ke gabatar da rahoton don tabbatar da matsayarsu, Shugaban kwamitin, Sanata Bala Ibn Na’Allah ya bayyana waɗansu saɗarori da suke ganin akwai buƙatar a soke su ko kuma a yi musu gyara.

Shugaban kwamitin ya ce sashe na 4(3) da na 4(4) sun cin karo da addinai da al’adun al’umma a Nijeriya, ya na mai cewa wajibi ne a soke su daga cikin ƙudirin.

Haka kuma ya bayyana rashin daidaito dake tattare da wasu layuka musamman waɗanda suke magana kan rabon kuɗaɗe da aka samu daga harajin da za a riƙa karɓa da wajen kowane ɓangare na al’ummar ƙasa.

By Babaji