Majalisa za ta yi karatu na biyu ga kasafin 2025 sa’o’i 24 bayan Tinubu ya gabatar da shi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun ɗage zama game da karatun ne zuwa ranar Talata, 14 ga watan Janairu, 2025 ga kasafin tiriliyan N49.7 da Shugaba Tinubu ya gabatar musuva ranar Laraba.

Kasafin ya tsallake karatu na farko ne Majalisar Dattawa bayan muhawara da aka gudanar ƙarƙashin jagoran sanatoci, Sanata Michael Opeyemi Bamidele da gudunmawar wasu guda 42.

Daga cikin abin da rabon kasafin ya ƙunsa akwai tiriliyan N4.4 ga harkokin gwamnati, sai N16.3tn na harkokin bashi, da na kashe-kashe tiriliyan N14.1; sai na gyare-gyaren kadarorin gwamnati 14.8 da sauran su.

An dai tsara kasafin ne la’akari da yadda farashin Dala take a kasuwa da kuma aikin samar da mai na ganga miliyan 2.06 a kullum.

Kasafin 2025 ya haura akan na baya da kaso 74.18 wanda hakan ya biyo bayan ƙalubale ne ga ayyukan ababen more rayuwa da na ci-gaba, kamar yadda Sanata Bamidele ya bayyana.

Baki ɗaya sanatoci 43 da ƴan Majalisar Wakilai da suka bada gudummawa wajen tantance kasafin, sun yaba da tsarinsa la’akari da amfanin da zai yi wa ƙasa da al’ummarta.

By Babaji