Sakin Nnamdi Kanu ba zai kawo ƙarshen rashin tsaro a Kudu Maso Gabas ba – Gwamnan Anambra

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, a ranar Talata, ya ce tabbas sakin jagoran ’yan awaren Biyafara, Nnamdi Kanu, da ake tsare da shi ba zai kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ta addabi yankin Kudu maso Gabas ba.

Soludo ya bayyana cewa, masu aikata laifuka suna saka rigar masu fafutukar kafa ƙasar Biyafara kuma a yanzu suna amfani da fafutukar ƙafa ƙasar Biyafara da sunan Kanu wajen aikata miyagun laifuffuka da rura wutar rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabas.

Soludo ya bayyana cewa, suna fakewa da biyafara, waɗannan mutane sun koma ga “ta’addanci,” suna yin fashi da makami, garkuwa da mutane, dabanci da bautar gumaka.

Ya dage cewa, ayyukansu ba shi da alaƙa da gwagwarmayar ‘yantar da gaskiya, yana mai cewa irin waɗannan laifuffuka ne kawai da ƙwadayi da rashin bin doka da oda.

Da yake jawabi yayin ganawa da manema labarai a gidan gwamna dake Amawbia a ranar Talata, Soludo ya bayyana cewa sama da kashi 99 cikin 100 na masu laifin da aka kama a Anambra a cikin shekaru biyun da suka gabata ‘yan ƙabilar Igo ne, inda sama da kashi 70 cikin 100 ba ’yan asalin jihar ba ne.

“Waɗanda ake kira masu tayar da hankali sun rikiɗe zuwa ƙungiyoyin masu aikata laifuka,” inji Soludo.

“Suna fakewa a cikin dazuzzuka, suna garkuwa da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, don neman kudin fansa, kuma suna kafa hujja da ta’addancin da suka aikata a bisa dalilin kafa ƙasar Biafra. Bari mu fayyace – wannan ba shi da alaƙa da duk wani yunƙuri na ‘yanci. Laifi ya ɗauki rayuwar kansa. Waɗannan mutanen sun ɗanɗana jini, kuma yanzu, kuɗi shi ne burin su.”

Gwamnan ya nuna shakkun cewa sakin shugaban ƙungiyar ta IPOB, Nnamdi Kanu, zai kawo ƙarshen rikicin, ganin yadda masu laifin suka yanke alaƙa da tunzura aka fara.

By ukarofi