
Daga BELLO A. BABAJI
Kawo yanzu jama’a ba su gani a ƙasa ba game da ragin farashin litar fetur da Kamfanin Ɗangote ya sanar da cewa ya yi a ƴan kwanakin nan zuwa N899.5 daga N970.
Mafi yawancin gidajen mai a Kano, Abuja, Fatakwal da Legas suna sayar da man ne akan N1,025 wanda shi ne mafi ƙarancin farashin kamfanin NNPCL sai kuma na manyan ƴan kasuwa da ke sayarwa a N1,070 da kuma N1,100 na ƴan kasuwa masu zaman kansu.
Kamfanin Ɗangote ya ce ya yi ragin ne don sauƙaƙe wa al’umma halin matsin da ake ciki a yayin bukukuwan ƙarshen shekara tare da yi musu godiya kan goyon baya da suke ba shi, kamar yadda Kakakinsa, Anthony Chiejina ya bayyana a makon nan.
Wani ƙwararre a harkar mai da ya buƙaci a sakaye sunansa ya ce farashin ɗanyen mai ya ragu a kasuwa daga sama da Dala 73 zuwa Dala 72 ga kowacce ganga wanda hakan dalili ne da ke nuna cewa farashin zai yi ƙasa da ma wasu dalilai.
