

Daga SARATU IBRAHIM MACHU
Da farko, Allah ya halicci mace ne don ta zama mataimakiya ga namiji wanda hakan ke nuna tana da rauni kuma ta na buƙatar kariya da tsaro ta kowacce hanya.
Cin zarafin ƴaƴa mata ya yi ƙamari a ƴan shekarun nan wanda ya kai ga har wasu matan sun rasa rayukansu a gidajen aure.
Idan rikici ya faru a garuruwa, mafi yawanci mata da yara ne suka fi jikkata.
Domin dakile cin zarafin mata a duniya baki ɗaya, Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) ta keɓe kwanaki 16 domin gudanar da shirye-shirye daban-daban na wayar da kan jama’a game da cin zarafin mata ƴaƴa mata.
‘Kawo ƙarshen cin zarafin mata da yara’, shi ne taken wannan shekarar inda ƙungiyoyi da dama masu zaman kansu da na ƙare haƙƙin ɗan-adam suka gudanar da shirye-shirye – kama daga wayar da kan jama’a har ya zuwa ga zagaye da jerin gwano ɗauke da kwalaye masu rubutu na kira ga al’umma baki ɗaya da a gujewa cin zarafin mata da yara a kowane yanayi.
Ambasada Yakubu Gam da Caroline Edward suna daga cikin waɗanda ƙungiyoyin Equal Access International da Mercy corps ɓangaren kula da haƙƙin mata da zaman lafiya a cikin al’umma suka yi wa koyarwa. Sun zayyano wasu matsaloli da suka shafi cin zarafin mata waɗanda suka haɗa da-
1-: Auren wurin mussaman ga yara matan da ba su Kai shekaru 18 ba.
2-: Auren Dole
3-: Hana mata gadon iyayensu
4-: Al’adun gargajiya da na addini da ke da cutarwa ga mata
5-: Nuna fifiko ga ƴaƴa maza fiye da mata.
6-: Rashin sa mata a harkar Siyasa da shugabancin gwamnati da na gargajiya.
7-: Fyaɗe, muzgunawa, cutarwa da rashin kula musaman a zamantakewar aure.

Ɗaya daga cikin waɗanda bala’in cin zarafin mata ya rutsa da ita wacce take zaune a jihar Filato, nan garin Jos a unguwar Rayfield ta yi bayyana cewa, mijinta ya tafi ya bar ta da ƴaƴa takwas kimanin shekaru goma kenan kuma an hana ta tashi domin ta sake wani auren. Ba ya aiko da abinci balle sutura ko kuɗin makarantar yara.
Akwai Kuma labarin yarinyar da wani mutum Ɗan shekaru 45 ya yi mata fyaɗe a unguwar Gyel da ke Ɓukuru a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu.
An yi nasarar damƙa shi ga ƴan sanda inda aka kulle shi amma daga bisani aka sako shi saboda masu faɗa-a-ji sun shiga maganar.
A watannin da suka gabata ne aka yi wa wata tsohowa duka wanda ya zama ajalinta a wata unguwa da ake kira Zawan bisa ga zargin ta da maita.
Haka ma cinikayyar yara mata wanda aka fi sani da trafficking a turance inda ake ɗibar yara mata akai wata ƙasar ko wani gari da sunan za su yi aiki amma kuma sai a tursasa su shiga karuwanci, da dai sauran munanan abubuwa da ake yi wa mata da yara.
An rinka samin tangarda daga wajen iyayen waɗanda aka ci ma zarafi saboda su na ƙin fitowa ko kin yarda su yi magana saboda gudun bacin suna.

Wasu kuma akan yi masu barazana da nuna masu ƙarfi wanda ake sa su dole su yi shuru, su kuma janye maganar fyaɗe ko cin zarafi daga kotu.
Akwai rashin bada haɗin-kai domin doka ta yi aikinta daga waɗanda abin ya shafa.
Sannan akwai kuma rashin kuɗi domin ɗaukaka ƙara da ga ɓangaren Wadanda aka cutar.
Haka ma akwai halin ko in kula daga ɓangaren jami’an tsaro da masu shari’a wanda daga ƙarshe ake sakin waɗanda aka kama da laifi kuma su cigaba da cutar da jama’a.



Akwai matsalar rashin isasshen wayar da Kai akan hanyoyin da ya kamata abi domin samun adalci.
Wasu dalilai da sukan jawo cin zarafin mata sune-:
Akwai matsalar talauci da rashin ingantacciyar kullawa daga iyaye wanda yakan jefa yara shiga halaye marasa kyau irin su shan ƙwayoyi saboda sun haɗa kai da muggan abokai.
Rashin zuwa Makaranta da rashin aikin yi ko sana’a.
Yanzu haka ƙungiyoyi masu zaman kansu tare da haɗin-gwiwar jama’ar da suka yi wa koyarwa sun cigaba da bada ƙaimi wajen yin bita domin wayarwa mutane kai akan illolin cin zarafin mata da yara.
Su na shirya koyarwa da tattaunawa da wayar da kan malaman makarantu, shugabannin gargajiya da ƙungiyoyin mata akan cin zarafin mata da yara.

Sannan wasu daga cikin jama’ar da aka yi wa koyarwa sun yanke shawarar koyar da mata da matasa sana’ar ɗinki da yin cake da girke-girke a unguwar Gyel da ke inda wasun su har sun gama koyon girke-girke sun karɓi shaidar kammalawa.
Shugaban ƙungiyar lauyoyi mata, FIDA, reshen Jihar filato Barista Misis Naankus Fyaktu ta bayyana cewa babban aikin kungiyar shi ne kare haƙƙin mata da yara daga kowane irin nau’i na cin zarafi, muzgunawa, cutarwa, lahani, cin mutunci da rashin kullawa a zamantakewar aure.
Su kan shigar da ƙara kotu don tabbatar da adalci, su kuma yi sulhu da sassanci a harkokin zamantakewar iyali, wanda kuma ya shafi barazana ga rayuwa da ya haɗa da duka har ya kai ga kisa a wasu lokuta sai a haɗa su da ƴan sanda domin gudanar bincike da shigar da ƙara a kotu.
Daga nan, mun tuntuɓi shugaban ƙungiyar ƴan jarida mata reshen jihar Filato, Misis Nene Dung domin jin irin rawar da suke takawa wajen tabbatar da an rage cin zarafin mata da yara. Ta kuwa yi bayani cewa sun haɗe kai da ƙungiyoyin irin su FIDA da Hukumar samar da Daidaito tsakanin Jinsi wato Gender Equality Commission da Equal Access international, da
saura ƙungiyoyi masu zaman kansu da ke kare haƙƙin ɗan-adam da bada kariya domin wayar da kan jama’a a tsarin shiye shirye da yada labarai bisa ga abubuwan da ke faruwa da kuma bin diddigi har sai an zartar da adalci.
Ta ƙara da cewa ta yi farin cikin matuƙa bisa rattaɓa hannu da gwamnati ta yi akan wasu tsarin dokoki da suke hani ga cin zarafin mata da yara da suka haɗa da:
1) Dokar tabbatar da adalci tsakanin Jinsi wato Gender Equal opportunities Law
2) Dokar kare haƙƙin Yara wato Child Rights Law da Kuma
3) Dokar Hana cutarwa ga Ƴan Adam wato Violence Against Persons Prohibition Law.
Waɗannan dokoki ne da suke amfani da su wajen gurfanar da masu laifi gaban hukuma.
Haka kuma shugabannin gargajiya sun shiga wannan gwagwarmaya ta yaƙi da cin zarafin ƴaƴa mata. Maga takarda na Mai garin Gyel Mr Jonathan DanGyang ya ce sun tattauna da masu unguwanni inda suka fitar da ta su tsarin dokokin masarautar su Wanda ta shafi hakkin mata Wanda yanzu haka wasu masarautun sun yi koyi da su don tabbatar da an bi wa mata haƙƙin su. Dokokin sune:
1) An haramta cin zarafin mata da Yara a masarautar Gyel Kuma duk Wanda aka kama da laifi zai fuskanci hukuma.
2) Duk wanda aka kama kuma aka tabbatar ya aikata laifin Fyaɗe, za’a zagaya da shi cikin unguwa tare da faɗin laifin da ya aikata sannan a Mika shi ga hukuma.
3) Yaya mata yanzu suna da damar su ci gadon iyayensu, duk Wanda aka kama da laifin handame dukiyar Yaya mata za’a sa shi ya biya Sannan ya fuskanci hukunci.
4) Wanda aka kama da laifin tursasawa mace Auren Dole mussaman ga diyar da ba ta Kai shekaru Sha takwas ba zaya fuskanci fushin hukuma da kotu.
Yanzu haka aƙalla Maza 120 ne suka Bada kansu wajen bincike da zakullo masu aikata Fyade a karkashin masarautar Gyel domin gurfanar da su gaban hukuma.
Ƙungiyoyin addini suma suna na su kokarin wajen dakile cin zarafin mata da Yara.
Shugaban ƙungiyar Jama’atul Nasarul Islam (JNI) kuma shugaban masu wa’azi sannan mataimakin limamin babban Masallacin Juma’a na karamar hukumar Jos ta Kudu Imam Idris Sani Auwal Sufi, ya ce suna ƙoƙarin wayar da kan jama’a a huɗubobinsu da kuma yin sulhu musamman a rayuwar zamantakewar aure.
Haka Revd. Dachung Tengwong wanda ke jagorantar kungiyar kristoci wato CAN yankin bukuru ya ce suna bin diddigi wajen tabbatar da cewa an yi adalci tsakanin Yara mata da Maza mussaman a harkar karatu da rabon gado.
Su na Kuma Kara wayer da kan jama’a da shirya koyarwa akan illolin cin zarafin mata da Yara.
Mataimakiyar shugaban karamar hukumar Jos south Hon. Mrs Kachollom Lucy Michael ta bayyana cewa gomnatin su a shirye ta ke domin ta ba mata dama a dama da su.
Akwai Kuma Shirin Bada tallafi da koyawa mata da matasa sana’o’i domin samin abin dogaro da Kai.
Yaran da suka daina zuwa Makaranta saboda matsalar rashin kudi mussaman na matakin firamare da na makarantun gaba da firamare za’a yi kokarin mayar da su Makaranta.
Sannan baya ga ofishin kula da walwalar al’umma na karamar hukumar, za’a Bada offishin kula da korafe korafe na kungiyoyi masu zaman kansu wato Desk officer a sabuwar shekarar nan domin karfafa aikin kungiyoyin.
Duk da irin ƙalubalantar da aka samu a yaƙi da cin zarafin mata da Yara, am sami nasarori da dama Wanda Com. Hamza Yakubu Mai fashion baki a harkokin Siyasar Najeriya ya zayyano su kamar haka- :
1) Shekara uku da suka wuce tsohon gwabna Simon Lalong ya rattafa hannu kan dokar Hana cin zarafin ‘ya-ya mata da Kare hakkin su bisa adalci. Hakan ya bada dama iyaye da al-umma da kungiyar Kare hakkin mata na kasa suyi anfani da ita don taimakawa gurin gurfanar da masu cin zarafin ƴaƴa mata da tauye hakkin su a zaman Aure .
Na biyu Mallaman Addinai na bada tasu gudumawa a cigaba da wayar da kan jama’a ta hanyar wa’azi da hudubobi.
Yawan Fyade da cin zarafin mata da Yara ya ragu sosai fiye da Kashi hamsin cikin Dari.
Yanzu doka ta ba mata damar da iya cin gadon iyayensu ba kamar da ba Wanda sai dai a rabawa yan’uwansu Maza kawai.
Yanzu masarautu sun fara sa mata a harkokin fada da shawarwari a harkokin da suka shafi al’umma. A fadar Mai garin Gyel kadai yanzu akwai Mata akalla su Tara da ke zuwa fada, Kuma Hakan ya Sami ne ta kokarin da kungiyoyi masu zaman kansu suka wajen bayyana alfanun sa mata a harkokin da suka shafi Mulki, shugabancin da sarauta.
An yi nasarar gurfanar da Wadanda suka aikata laifin Fyade gaban kuliya da dama Wanda yanzu haka wasunsu suna gidan kaso wasu Kuma suna hannun Yan Sanda ana gudanar da bincike. Yanzu haka akwai Wanda ya shiga hannun Yan Sanda a kayen Riyom bisa laifin aikata Fyade.
Ɗan sandan da ya katsewa matar hannu kuma shi ma yana hannun hukuma.
Gwamnatin jihar filato ta Sami damar ceto wasu daga cikin Yan matan da aka Kai Ghana da Mali da Kuma wasu jihohin cikin gida Najeriya da sunan yin aiki amma ana azabtar da su da tursasa masu shiga karuwanci.
Daga karshe gwamnati da ita wannan kungiyar ta majalisar dikin duniya su Kara kaimi wurin wayar da Kan al-umma dan su kawo korafe-korafensu don daukar mataki na rage irin wannan hali daga cigaba.
Sannan duk jami’in da aka kama da aikata rashin adalci ko halin ko in kula mussaman a harkar da ta shafi cin cin zarafin mata da Yara a gurfanar da shi gaban hukuma domin ya zama darasi ga masu irin wannan halin.
