Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Raya ƙasa ta Babban Birnin Tarayya, Abujƙ, ta rusa tashoshin da ba su da izini a Apo Zone E, gundumar Gudu, Abuja.
Hukumar ya kuma rusa wani wurin kwanan ’yan cirani da suke zama ba bisa ƙa’ida ba a gundumar.
Daraktan hukumar, Mukhtar Galadima, ya bayyana hakan a yayin atisayen a Abuja ranar Talata, cewa an gina wuraren ne ba tare da amincewar gwamnati ba.
Galadima, wanda yake wurin da abin ya faru tare da jami’an hukumar, ya bayyana cewa, gine-ginen babban cin zarafi ne ga tsarin Abuja.
Ya bayyana cewa, an ruguza wurare ne saboda faɗaɗa gine-ginen birnin.
Ya ƙara da cewa, haramtattun wuaren da aka gina, shi ma ya hana magudanar ruwa, wanda idan aka amince da su, zai iya haifar da zaizayar ƙasa da ambaliya.
Ya bayyana cewa, an gano haramtattun gine-ginen ne a yayin ziyarar mako-mako na sashen na duba abubuwan da ke faruwa a birnin tarayya.
“A ziyarar da muka saba yi na mako-mako a yau a Apo Zone E, gundumar Gudu, mun gano abubuwan ban mamaki a yankin.
“An gina gine-ginen a wasu wurare da ya kamata ruwa ya wuce don haka dole ne mu dakatar da aikin.
“Za mu ci gaba da sanya ido kan abubuwan da ke faruwa, kuma duk wani mai haɓaka ba bisa ƙa’ida ba wanda ya ki dakatar da ci gaba ba tare da izini ba, za a kama shi.
“Sauran gine-ginen da aka kammala kuma za a ruguje su,” in ji daraktan.
A nasa ɓangaren, daraktan kula da wuraren shakatawa da shakatawa Chinemelu Echee, ya ce hukumar za ta kwato duk wuraren da aka kori da aka yi amfani da su.
