Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Tsohon gwamnan Jihar Zamfara kuma ƙaramin ministan tsaro, Bello Muhammad Matawalle ya yabawa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan matakin da ta ɗauka na dakatar da dokar hana haƙar ma’adinai a ƙasar nan cikin gaggawa.
Matawalle ya yi wannan yabon ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a gidansa da ke Gusau a jiya.
A cewar sa, matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na ɗage haramcin haƙar ma’adanai, abu ne mai kyau, a cewar shi matakin zai bunƙasa tattalin arzikin jihohin da Allah ya albarkace su da albarkatun ma’adinai a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya musamman Jihar Zamfara.
Jaridar Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na ɗage dokar dakatar da haƙo ma’adanai na zuwa ne bayan shekaru biyar da tsohon shugaban ƙasa Muhamadu Buhari ya haramta duk wasu ayyukan haƙar ma’adanai a sakamakon matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma.
Minista Matawalle ya bayyana cewa ɗage haramcin aikin haƙar ma’adinai zai inganta tsaro sosai domin da yawa daga cikin ‘yan Nijeriya za su samu hanyar rayuwa da bunƙasar tattalin arzikin su.
Ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya ta duƙufa wajen ganin ta shawo kan matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin Arewa maso Yamma da sauran jihohin ƙasar nan a sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda masu ɗauke da makamai domin dawo da zaman lafiya.
“Mai girma shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana yin duk mai yiwuwa wajen ganin an magance matsalar rashin tsaro da ya addabi wasu jihohin Arewa, kuma da ikon Allah maɗaukakin sarki, ƙarshen ‘yan ta’addan zaizo nan bada jimawa ba, la’akari da yadda jami’an tsaron mu ke ƙoƙarin ganin an daƙile su a duk inda suke.
Matawalle ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su marawa gwamnatin tarayya baya domin ganin an kawo ƙarshen ‘yan ta’adda musamman jihohin da ayyukan yan ta’adda suka shafa a Arewacin ƙasar nan.
