Duk wanda zai kawo tashin hankali a Jihar Kano ba masoyin mu ba ne – AVM Ibrahim

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

An bayyana cewa dukkan wanda zai kawo tashin hankali a Jihar Kano ko Ƙasar nan ba masoyin da za’ayi alfahari da shi bane a cikin Al’umma.

Babban darakta na ayyuka na musamman a fannin tsaro AVM Ibrahim Umar(Rtd) ne ya bayyana haka yayin wani sulhu da ya jagoranta a cigaba da faɗan daba dake wanzuwa a anguwannin Zage,Ƙofar Mata,Yakasai da Zango da sauran wasu yankuna dake cikin birnin Kano.

AVM ya ce a wannan gwamnati ta Gwamna Abba Kabir Yusuf kowa yasan irin ƙoƙarin da ta ke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma don cigaban Kano a halin yanzu.

”Ya zama dole mu taimakawa mai girma gwamna Abba Kabir saboda mu ke wakilan shi dake unguwanni da sauran wanda abin ya shafa dan samar da zaman lafiya a wannan jiha tamu.

”Dan haka yau mun kira ku ne domin jan kunnuwan ku kan wannan rikici dake wanzuwa, dan babu abinda yafi zaman lafiya da kwanciyar hankali,dan haka ku rungume shi.

Ibrahim Umar ya ƙara da cewa yanzu ne yakamata ace matasa sun mai da hankalin su wajen tsayawa kan turbar da ta dace wadda za ta taimaki rayuwar su kamar yadda koda yaushe mai girma gwamna yake fata.

”Amma ku sani gwamnati ba za ta cigaba da lamuntar faɗace-faɗacen daba ba da uzurta ma al’ummar Kano har ta kai ga rasa rayuka ko dukiyar su, lallai gwamnati za ta iya ɗaukar matakin ladabtarwa ta kowace sigar da ta ga dama.”

”Kan batun zaman da mu ka yi kuma yau Alhamdullahi, da mu da masu unguwanin ,da su kan su matasan an samu matsaya guda ɗaya da kuma murya ɗaya.”

Ya cigaba da cewa, matasan sunyi alƙawarin cewa daga yau sun ajiye makamin su babu su babu faɗan daba a wannan yanki nasu, inda ya ƙara da cewa gwamnati a shirye take wajen ganin ta taimaka masu da dukkan abinda yakamata.

Da suke nasu jawabin wasu daga cikin shugabanin matasan da suka halarci zaman sulhun sun ce daga yau sun ajiye makaman su tare da rungumar nasihar da gwamnatin Kano ta shirya.

Sai dai sun buƙaci cewa gwamnati ta kira ɗaya ɓangaren dan suma a zauna dasu tare da yin irin wannan zaman dan Kawo ƙarshen zaman.

Sai dai sunyi tsokaci akan cewa rashin aikin yi da nuna halin ko in kula lokaci da dama da ake nuna masu ne yake sawa da yawansu canzawa daga yanayin da aka san su dashi na kamewa daga aikata wasu ayukan da basu da kyau.

By ukarofi