A ranar Litinin, 24 ga watan Disamba, 2024, an sami rahoto cewa wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai hari kan sansanin sojoji da ke Damboa, a Jihar Borno.
Bisa bayanan da Blueprint ta tattara, harin ya auku ne da yammacin daren Kirsimeti, lokacin da jiragen yaƙi marasa matuki, ɗauke da bama-bamai, suka kai farmaki kan sansanin sojojin.
Aƙalla sojoji shida sun samu raunuka sakamakon harin, kuma an basu agajin gaggawa a wajen kafin a ɗauke su zuwa ga asibiti domin ƙarin kula.
Harin ya fara ne da harbe-harbe daga masu tayar da ƙayar baya, wanda sojojin suka daƙile cikin lokaci. Sai dai, bayan wannan fafatawar, jiragen yaƙi dauke da abubuwan fashewa sun sake kai farmaki kan sansanin, inda suka jefa bamabamai a cikin wurin.
A halin yanzu, jami’an tsaro suna ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin domin tabbatar da tsaron yankin.
