
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika da saƙon ta’azzarsa ga Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Maryam Namadi.
A safiyar ranar Laraba ne marigayiyar ta rasu, wadda aka yi jana’izarta a garin Kafin Hausa inda nan ne mahaifar gwamnan.
NAN ya ruwaito cewa, wata sanarwa daga Fadar shugaban ƙasa ta ce Shugaba Tinubu ya yaba da irin ƙoƙarin da marigayiyar ta kasance tana yi wa al’umma na kyautatawa sadaukarwa inda ya yi kira ga iyalanta da su cigaba daga inda ta tsaya.
Shugaban ya kuma yi kira ga gwamna Namadi da sauran iyalan nata da su kasance masu haƙuri da juriya bisa babban rashin tare da mata addu’ar fatan samun rahamar Allah.
