KAROTA ta gurfanar da mutane uku da ake zargi da cin zarafin jami’anta

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Hukumar kula da zirga zirgar ababen hawa ta Jihar Kano KAROTA, ta gurfanar da wasu mutane uku, da ake zarginsu da cin zarafin jami’anta yayin da suke tsaka da gudanar da aikinsu.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta KAROTA Nabulisu AbubakarK/ Na’isa ya aikewa manema labarai yace, waɗanda hukumar ta gurfanar gaban kotun sun haɗa da Abubakar Mustapha, Najib Idris, da kuma Faruk Ɗan Alhaji

An dai gurfanar da waɗannan mutane a gaban kotun Nomanslands mai lamba 47, dake unguwar Sabon Gari.

Bayan gurfanar da mutanen da ake zargin a gaban kotun, alƙalin kotun ya karanto musu tuhumar da ake yi musu na hana jami,an hukumar gudanar da aikinsu wanda ya saɓa da sashi na 79, da kuma sashi na 171 da 242 haɗi da sashi na 327 na kundin penal code.

Kazalika alƙalin kotun mai zaman nata a Nomanslands ya aike da mutane biyun da suka zo hannu wato Abubakar Mustapha da Najib Idris, tare da bayar da umarnin kamo Faruok Ɗan Alhaji, wanda kotun ke nema ruwa a jallo.

Alƙalin kotun ya ja kunnen jama’a da su guji aikata irin wannan abu ga Jami’an tsaro, tare da jan kunnen jami’an hukumar KAROTA da su ringa nuna kwarewa yayin da suke gudanar da aikinsu, kamar yanda kundin dokar hukumar ta tanada.

Daga nan sai shugaban hukumar ta KAROTA Hon. Faisal Mahmud Kabir ya nuna gamsuwarsa da yanda Shari’ar ta gudana, tare da yin kira ga Jama’a da su kaucewa daukar doka a hannunsu, idan wani sabani ya faru tsakaninsu da Jami’an hukumar ta KAROTA.

By ukarofi