Gwamna Abba ya ƙaddamar da cibiyar kula da masu cutar Sikila kyauta a Kano

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

A wani mataki mai ƙarfi don yaƙar ciwon Amosanin Jini, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da wata sabuwar cibiyar lafiya mai inganci da za ta riƙa bayar da kulawa ta musamman kyauta ga masu fama da wannan cuta.

Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin Kwamishinan Lafiya, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, yayin bikin ƙaddamar da makon kula da lafiyar uwa da jariri na biyu a shekarar 2024 a ƙaramar hukumar Kumbotso.

Sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta bayyana cewa cibiyar kulawar ta musamman tana cikin Asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad.

Cibiyar za ta bayar da ayyuka masu yawa kyauta, waɗanda suka haɗa da gwaje-gwaje, shawarwari, bayar da magunguna, da kuma gudanar da ayyukan tiyata ga masu fama da ciwon Sikila.

Gwamna Yusuf ya dage wajen yaƙi da matsalar ciwon sikila ne bisa alƙawuran da ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓensa, kamar yadda aka bayyana a cikin tsarinsa na gyaran harkar lafiya.

A farkon shekarar nan, Gwamnan ya sanya hannu kan wani muhimmin ƙudirin doka na gwajin lafiya kafin aure, wanda ya haramta auratayya tsakanin masoya da suke da irin wannan nau’in ƙwayoyin halitta (genotype) a jihar, domin hana haihuwar ‘ya’ya da ciwon Sikila.

By ukarofi