Gwamnan Kebbi ya karrama ɗan Kano, Sanusi Idris, wanda ya yi na ɗaya a gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamnan Jihar Kebbi, Malam Nasir Idris, ƙauran Gwandu, ya karrama Malam Buhari Sanusi-Idris daga Jihar Kano a matsayin gwarzon shekara a gasar karatun Al-ƙur’ani ta ƙasa karo na 39 da aka gudanar a Birnin Kebbi.

Hajiya Zainab Nasare Nasir Idris, matar gwamnan, ta kuma karrama Malama Rumaisa’u Ɗahiru Ibrahim daga Jihar Gombe a matsayin zakaran ɓangaren mata. Duka sun samu kyautar motar hawa, kujerar aikin hajji, Naira 500,000 da kuma talabijin plasma, yayin da Rumaisa’u ta ƙara samun kyautar firji.

Wannan gasa, wadda aka shirya domin zaɓen wakilai da za su wakilci Nijeriya a gasar karatun Al-ƙur’ani ta duniya, ta samu mahalarta daga jihohi 35 na tarayyar Nijeriya, inda maza 125 da mata 113 suka fafata a rukuni guda shida tsawon kwanaki takwas.

A wajen bikin rufe gasar da aka yi a makarantar Umar Waziri Federal Polytechnic, gwamna Idris ya bayyana farin cikinsa kan damar da aka ba Kebbi ta karɓar baƙuncin wannan muhimmiyar gasa, yana mai yaba wa hazaƙar mahalarta wajen haddace Al-ƙur’ani mai girma.

Gwamnan ya jaddada niyyarsa na ci gaba da tallafa wa addinin musulunci, inda ya bayyana cewa ana ci gaba da aikin sake gina masallatai 400 a faɗin jihar.

Har ila yau, ya yi kira ga al’umma da su fahimci hikimar karatun Al-ƙur’ani wanda yake koyar da tausayi, ladabi, da kuma zaman lafiya a tsakanin bil’adama.

A jawabinsa, Shugaban Kwalejin Usman Danfodio ta Sokoto, Farfesa Bashir Garba, ya yaba wa dukkan mahalarta gasar, yana mai cewa an cimma manufofin gasar. Haka zalika, Sheikh Abdullahi Bala-Lau, shugaban JIBWIS, ya bayyana Al-ƙur’ani mai girma a matsayin albarka ga mutane, yayin da Sheikh Ibrahim Ɗahiru Bauchi, mai wakiltar Sheikh Ɗahiru Bauchi, ya yi kira ga al’umma da su rungumi koyarwar Al ƙur’ani da kuma neman taimakon Allah wajen shawo kan matsalolin ƙasa.

By ukarofi