Shugaba Tchiani na fuskantar suka daga ƴan Nijar bisa zargin Nijeriya da yi wa ƙasar maƙarƙashiya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaban mulkin sojin Jamhuriyar Nijar, Abdurrahman Tchiani na fuskantar suka daga wasu ƴan ƙasar kan zargin Nijeriya da shirya wa Nijar maƙarƙashiya.

Daga cikin abin da shugaban ya faɗa a yayin wata hira da shi a ranar Kirsimeti, ya ce Nijeriya ta samar da sansanin sojojin Faransa a yankin tafkin Chadi da sansanonin horar da ƴan ta’adda a jihohin Sakkwato, Zamfara da Kebbi don haddasa tashin-tashina a Nijar.

Saidai, Gwamantin Tarayya ta ofishin Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkar tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu ta ƙaryata zargin inda ta ce batu ne mara asali dake neman haifar da sa-insa tsakanin ƙasashen biyu.

Mutane da dama ta kafafen labarai sun yi ta tsokaci game da batun tare da samun kushewa daga gare musamman a Soshiyal Midiya ganin cewa babu ƙamshin gaskiya acikinsa.

Wasu na ganin hakan a matsayin rufa-rufa daga shugaban na Nijar bisa gazawarsa a ƙaragar mulki tun bayan hamɓarar da Shugaba Mohamed Bazoum watanni 17 da suka gabata.

By Babaji