Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bai wa iyalai da suka rasa ‘yan uwansu a harin da sojoji suka kai a ƙananan hukumomin Silame da ke Jihar Sokoto hakuri. Harin, wanda ya faru a ranar Larabar 25 ga watan Disamba, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 yayin da sojoji suka kai hari kan sansanin ’yan ta’addan Lakurawa a wasu ƙauyukan yankin.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha, ya fitar, Shettima ya bayyana jimaminsa kan wannan al’amari mai ɗaure kai, inda ya ce wannan wani lokaci ne na baƙin ciki da aka samu asarar rayukan fararen hula yayin yunƙurin magance ta’addanci. Ya ce, “Muna ba da haƙuri tare da nuna alhini ga waɗanda suka rasa ‘yan uwansu a wannan hari, wanda ya haifar da mummunan raɗaɗi ga iyalai da al’ummar Silame.”
Shettima ya kuma roƙi al’umma da su fahimci cewa irin waɗannan al’amura ba su saba faruwa ba, kuma baƙin cikin gwamnatin tarayya kan faruwar hakan ba zai misaltu ba. Ya jaddada cewa sojojin Nijeriya suna bayar da rayukansu ne don kare al’umma daga hannun ’yan ta’adda, kuma wannan aiki ba zai samu nasara ba sai da haɗin kan jama’a.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce gwamnatin tarayya, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, za ta ci gaba da tallafa wa iyalan mamatan da kuma tabbatar da cewa an kawar da ƙungiyoyin ta’addanci daga ƙasa baki ɗaya. Ya kuma yi kira ga al’umma da su bayar da bayanai masu amfani da za su taimaka wa sojoji wajen bambance ‘yan ta’adda da fararen hula.
A ƙarshe, Shettima ya tabbatar wa al’ummar Jihar Sokoto cewa gwamnatin tarayya ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro a Nijeriya. Ya ce haɗin kai da goyon bayan jama’a zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasa baki ɗaya.
