Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A yayin da nake wannan rubutu, mabiya addinin Kirista a ko ina a faɗin duniya suna cikin hidimar bukukuwan Kirsimeti, wanda ake yi duk shekara a daidai irin wannan lokaci na ƙarshen shekara, domin tunawa da haihuwar Yeso Almasihu.
Gab da lokacin Kirsimeti kamar yadda aka saba masu hali da ƙungiyoyin sakai da majami’u, musamman ma ‘yan siyasa, suna shirya taruka don rabon abinci da sutura ga mabuƙata da marayu ko gwagwaren mata da suka rasa mazajen su. Ana haka ne da nufin taimaka musu da abin da za su ci abinci da iyalinsu, cikin farinciki da walwala, kamar yadda Musulmi kan yi a lokutan azumi ko Sallah.
Ba da tallafi ga mabuƙata da masu rayuwa cikin ƙunci kamar ‘yan gudun Hijira, marayu, tsofaffi da nakasassu abu ne da kowanne addini ke ƙarfafa gwiwar a yi, saboda alherin da hakan ke da shi. Ba ma a addinance ba ko da a tsari na mutumtaka kyautayi da tallafawa mabuƙata abu ne mai kyau. Inda ake da matsala da hakan shi ne idan aka yi rabon ba bisa tsari ba, yadda zai jefa rayuwar jama’a da dama cikin haɗari, kamar yadda abin da ya faru a makon da ya gabata.
Rahotanni sun bayyana cewa kimanin mutane 67 ne suka rasu ciki har da ƙananan yara, yayin da wasu da dama suka jikkata, a tarukan rabon abinci da aka samu turmutsitsi, a jihohin Oyo, Anambra, da Babban Birnin Tarayya Abuja. Aƙalla yara 35 ne suka rasu a Jihar Oyo, yayin da mutane 22 suka rasa rayukansu a Anambra, sai kuma wasu ƙarin rayuka 10 da aka rasa a Abuja.
Yawanci duk sun rasa rayukansu su ne a yayin jerin gwanon rabon abinci da sutura da aka shirya rabawa, don tallafawa mambobin majami’a da maƙwafta da ke rayuwa cikin ƙuncin rayuwa. Duk da tsarin da aka yi, a wasu daga cikin wuraren sai da cincirindon jama’a ya rinjayi masu kula da tsarin rabon kayan abincin.
Aukuwar wannan ibtila’i da asarar rayuka da aka fuskanta ya ɗaga hankalin jama’a da dama, musamman makusantan waɗanda suka rasu, da masu shirya rabon, da suka yi tunanin ba da tallafin da kyakkyawar niyya, amma ƙaddara ta faɗa wa shirin. Kodayake gwamnatin tarayya da hukumar ’yan sanda sun kafa kwamitocin bincike, domin gano musabbabin aukuwar turmutsitsin, amma manazarta da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum, na nuni da cewa abin da ya faru shaida ce da ke ƙara tabbatar da cewa ana yunwa a ƙasa. ‘Yan Nijeriya na fama da matsalar tattalin arziki, tsadar rayuwa ta tilasta mutane shiga ƙunci da rashin wadatar abinci. Abin da jama’a suka fi buƙata yanzu shi ne abinci.
Manazarta harkokin tattalin arziki na ɗora alhakin halin ƙaƙa nikayi da ’yan Nijeriya ke ciki kan tsare-tsaren Gwamnatin Tarayya. Wani masanin tattalin arziki, Haɗi Saleh ɗankishiya, ya bayyana cewa, tun da gwamnati ta janye tallafin man fetur da na wutar lantarki, rayuwar ‘yan Nijeriya ta ƙara shiga ƙunci da tsadar al’amura. Cefane da kula da hidimar iyali ta gagari talakan Nijeriya da masu ƙaramin ƙarfi.
Ya ce, duk da rahoton da Hukumar ƙididdiga ta Ƙasa ta fitar da ke nuna ana samun farfaɗowar tattalin arziki hakan ba wani sauyi da zai iya kawowa wajen canza farashin kaya a kasuwa. Bilhasali ma sai hauhawa farashi ke ƙara yi, yayin kayan abinci ke cigaba da canza farashi hatta a kasuwannin ƙauyuka, inda a baya ake ɗan samun sauƙin kayan abinci.
Na je aiki wani ƙauye, inda wani ɗan siyasa ya shirya rabon shinkafa da kayan abinci ga tsofaffi da matan da suka rasa mazajen su. Kodayake, ba a samu cinkoso da turmutsitsi a wajen ba, amma wasu kalamai da wani daga cikin manyan baƙi ya faɗa wa matan shi ne ya fi ɗaukar hankalina. Abin da ya gaya musu kuwa shi ne, duk da kasancewar su manoma ne kar su yi gaggawar sayar da kayan amfanin gonakinsu, saboda halin da ake ciki yanzu a ƙasar nan, ana ƙara fuskantar yunwa ne. Idan suka sayar da kayan gonarsu da wuri, za su zo suna awu da ƙyar, babu kuɗin saye.
Wannan gaskiya ne. Idan ba da tallafin ubangiji ba, akwai yiwuwar wahalar da jama’a ke ciki ta tsadar kayan abinci da ƙarancinsa za ta jima ana fama da ita. Saboda yadda manyan ’yan kasuwa suke saye abincin a manyan motocin ɗaukar kaya, daga kasuwannin ƙauye, don adanawa a manyan wuraren adana kaya, ko sayarwa ga manyan kamfanonin sarrafa kayan abinci. Don haka dole abinci ya yi ƙaranci da tsada a ƙasar nan.
Kimanin kashi 63 cikin ɗari na ‘yan Nijeriya miliyan 210 na fuskantar da yunwa da matsalar tsadar abinci. Wannan babban abin tashin hankali ne matuƙa, ga duk wani shugaba da ɗan ƙasa nagari mai tunani da hangen nesa. Kodayake, gwamnati da Hukumar ‘Yan sanda ta ƙasa sun bayar da umarnin tilas duk inda za a yi wani taron kayan abinci ga talakawa, sai an sanar da su don su san tsarin da za a yi a kaucewa samun turmutsitsi, amma akwai alamun in dai Gwamnatin Tarayya da na jihohi ba su ɗauki ƙwararan matakai na yaƙi da yunwa da tsadar rayuwa ba to, kuwa akwai sauran turmutsitsi.
Yana da kyau Gwamnatin Tarayya ta ƙara faɗaɗa shirin ta na yaƙi da talauci ta hanyar tallafawa manoma da jari mai kauri, a farfaɗo da ƙananan masana’antu da harkokin kasuwanci da ba su da alaƙa da man fetur. A maimakon a riƙa rabon shinkafar da bai wuce mudu biyu zuwa uku a matsayin yaƙi da talauci, wanda ba ya maganin komai, kamata ya yi a ɓullo da tsarin koyar da sana’o’in dogaro da kai, da zai zama mataki-mataki, kuma mai ɗorewa.
A ƙarfafa tsarin koya wa ɗalibai sana’o’i da fasahohin zamani tun daga makarantun sakandire zuwa jami’o’i, domin su iya dogaro da kansu kafin su gama makaranta. Ta yadda za su cire tunanin su daga samun aikin gwamnati. Gwamnati ta zuba jari da sa’ido kan harkokin ma’adinai, domin samar da ƙarin hanyoyin shigar kuɗaɗe hannun jama’a, samar da ayyukan yi, da magance tsadar rayuwa.
