Sojoji sun kama wacce ke yi wa Bello Turji safarar alburusai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Dakarun tsaro na atisayen ‘Fansan Yamma’, sun yi nasarar kama wata Shamsiyya Ahadu mai shekaru 25 bisa laifin safarar alburusai.

Kakakin dakarun, Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

A ranar 28 ga watan Disamba ne aka kama Shamsiyya tare da mai mashin ɗin da ya ɗakko ta mai suna Ahmed Husaini a yankin Badarawa dake ƙaramar hukumar Shinkafi a jihar.

An kama ta ne ɗauke da wasu alburusai guda 764 ƙirar 7.62mm da wasu mujallu shida da nufin kai wa sanannen jagoran ƴan bindiga, Bello Turji.

Sanarwar ta ce an kama mai laifin ne bayan wani rahoton sirri game da kayayyakin ayyukan ƴan ta’adda da aka yi dakon su daga yankin Kware zuwa Badarawa.

Ta ƙara da cewa, a halin yanzu hukumomi suna cigaba da gudanar da bincike akan waɗanda aka kama.

By Babaji