
Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya taya Buhari Idris murnar nasarar lashe gasar karatun Al-ƙur’ani mai girma ta ƙasa da ta gudana a ranar Asabar wadda ita ce karo na 39.
Gwamna Abba ya miƙa sakon ne ta cikin wata sanarwa da Daraktan yaɗa labaransa Malam Sanusi Bature ya fitar, wanda ya ce Buhari ya samu nasara ne da maki 98.2 kan abokan karawarsa.
Gasar, wadda ta gudana a birnin Kebbi, babban birnin jihar kebbi, ta samu halartar manyan malamai da ɗalibai daga ciki da wajen Najeriya.
Sanarwar ta ce da yake bayyana farin cikinsa yayin samun labarin nasarar da ɗan asalin jihar ta Kanon ya samu, gwamnan ya bayyana ƙudirinsa na haɗa masa liyafa da kujerar Hajji tun lokacin da ya samu nasara a matakin Jiha.
Gwamnan ya kuma ƙara bugun kirji da alfahari da cewa jihar Kano nan ne Gidan Alqur’ani, ta re da fatan ta cigaba da zama a kan gaba wajen cigaba da zama jihar tallafawa wajen damar karatun addini.
”Mu na amfain da wannan dama domin ƙarfafa maka gwuiwa wajen cigaba da amfani da abinda ƙur’ani yake koyarwa.
Gwamna Abba ya kuma yi kira ga sauran al’umma da su ƙara taya Najeriya da addu’ar samun lafiya da haɗin kai gami da koyi da karantarwar ƙur’ani don samun haske da tsira hadi da mafita a harkokinsu na yau da kullum.
