
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar, ya yaba wa jami’an tsaro bisa jajircewarsu wajen daƙile ayyukan ƴan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma, yana mai cewa, ƙoƙarin da suke yi zai bai wa kaso 85 bisa 100 na manoma damar koma wa gonakinsu a damina mai zuwa.
Ya faɗi hakan ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai a gidansa dake Garin Talata Mafara a ƙaramar hukumar Talata Mafara, a ranar Asabar.
A cewarsa, sannu a hankali zaman lafiya yana dawowa sakamakon ba-takashi da sojoji ke yi da ƴan ta’adda a Jihar Zamfara da sauran jihohin da ayyukansu ke addaba a Arewa maso Yamma.
“Ya zuwa yanzu, tare da jajircewar da sojoji da sauran jami’an tsaron ƴan uwa suka yi wajen yaƙi da ƴan ta’adda, za a magance matsalar ƴan ta’adda nan bada jimawa ba,” inji shi.
Sanata Yari ya kuma yaba wa Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bisa nuna damuwa da jajircewa wajen magance matsalar rashin tsaro da ya addabi yankin.
“Hakika shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana bakin kokarinsa wajen ganin an dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma kuma za mu cigaba da ba shi goyon baya domin cimma burin da ake so ta wannan bangaren.”
Ya buƙaci al’ummar Zamfara da Arewa maso Yamma da su cigaba da yi wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu addu’ar samun nasara musamman akan batun magance matsalar rashin tsaro a yankin.
