

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Dakarun Birget ta ɗaya, tawaga ta 2 a atisayen ‘Fansan Yamma’, sun kama wata ‘yar shekara 25 mai suna Shamsiyya Ahadu ɗauke da harsashi na musamman samfurin 764mm 7.62mm da kuma kenson harsasai Gida shida (Magazine 6) a yunƙurin ta na kaiwa sansanin ‘yan ta’addan Bello Turji.
Kodinetan Joint Media Coordinating Center Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Gusau, inda ya ce an kama Shamsiyya ne a ranar 28 ga watan Disamba, 2024 tare da abokinta, wani direban babur mai suna Ahmed Husaini a yankin Badarawa a ƙaramar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.
Ya ce kama su ya biyo bayan rahoton sirri da aka samu ne game da zirga-zirgar kayan aikin ‘yan ta’addan a kan hanyar Kware zuwa Badarawa a ƙaramar hukumar ta Shinkafi ta jihar Zamfara.
“Sakamakon ci-gaban da aka samu, dakarun Operation Fansan Yamma sun yi gaggawar kafa shingen bincike wanda ya kai ga cafke waɗanda ake zargin.”
Ya bayyana cewa, a halin yanzu dukkan waɗanda ake zargin ana ci gaba da binciken su don miƙa su ga hukumar da ta dace don su fuskanci hukunci.
Laftanar Kanar Abubakar ya ƙara da cewa, aikin na Fansan Yamma da rundunar sojin ke yi zai cigaba da himma wajen tarwatsa duk wata kafar sadarwa ta ‘yan ta’adda tare da hana zirga-zirgar makamai da alburusai a duk faɗin jihar.
“Don haka mu na kira ga jama’a da kada su yi ƙasa a gwiwa wajen samar da sahihin bayanan da za su kai ga kamo ‘yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo da kuma abokan hulɗarsu”, inji shi.
“Bugu da ƙari, rundunarmu tana yaba wa da irin goyon bayan da al’ummar yankin ke bayarwa gare mu na cigaba da gudanar da aikin Operation Fansan Yamma cikin nasara.”
