Kwananka ya kusa ƙarewa – Hedikwatar Tsaro ga Bello Turji

Spread the love

Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana cewa shugaban ‘yan ta’adda mai suna Bello Turji, wanda kwanan nan ya yi barazanar kai hari a wasu ƙauyukan jihohin Zamfara da Sakkwato idan aka ƙi sakin ɗan uwansa da wasu da sojoji suka kama a matsayin wanda kwanan shi suka kusa ƙarewa.

Wannan furuci ya zo ne yayin da rundunar ta caccaki masu ƙalubalantar luguden bama-baman da aka kai a sansanin ‘yan ta’adda na Lakurawa a ranar Kirsimeti.

Babban Janar Edward Buba, daraktan ayyukan hulɗa da jama’a na tsaron Ƙasa, ya ce, “Tun daga watan Janairu zuwa yau, 31 ga Disamba 2024, an kashe fiye da shugabanni da kwamandojin ‘yan ta’adda 1,000 da kuma waɗanda suka maye gurbinsu.

Wannan abu ne da zai faru da sauran ‘yan ta’addan, ciki har da Bello Turji. Gaskiya, Bello Turji matacce ne kawai da ke tafiya. Bai kamata a shiga muhawara da shi ba, domin kafin shi, akwai wasu ‘yan ta’adda da suka yi irin wannan barazanar. Amma yau duk an kawar da su.”

Janar Buba ya tabbatar da cewa rundunar soji ta kashe da dama daga cikin ‘yan ta’adda a fagen fama, yana mai cewa sauran waɗanda suka rage, ciki har da Bello Turji, suna gab da gamuwa da irin wannan makomar. Ya ƙara da cewa, “Mun binne da dama daga cikin su a filin daga domin wannan ne ƙarshen su.”

Dangane da masu ƙalubalantar luguden bama-baman da aka kai a sansanin ‘yan ta’adda na Lakurawa, Janar Buba ya ce, “A lokacin yaƙi, gaskiya ake fara ruguzawa . Saboda haka, ba abin mamaki ba ne idan ‘yan ta’adda ko masu goyon bayansu suka yi maganganun da ba su dace da gaskiya ba. Wannan dai ya zama hanyar ƙage domin su rage tasirin abin da muka yi musu.”

Ya kuma ja kunnen al’umma kada su bari irin wannan ƙage ya yi tasiri, yana mai cewa, “Wannan yaƙin Nijeriya ne na ‘yan Najeriya. ‘Yan ta’adda ba sa farin cikin yadda muka rusa musu kayan aiki da sansaninsu. Kada ku bari su yaudare ku da farfagandar su. Za mu ci gaba da yaƙi har sai mun kawar da sauran shugabanninsu.”

By ukarofi