Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A ƙoƙarin da ta ke na bunƙasa sha’anin kiwon lafiya a jihar, gwamnatin Katsina ta ɗauki ƙarin sabbin ma’aikatan kula da lafiya 254.
Mataimakin gwamnan jihar Farouk Lawal Joɓe ya faɗi haka a hira da manema labarai da ya yi a Katsina.
Ya bayyana cewa tuni ma aka tura su aiki a manyan asibitoci da ke faɗin jihar domin kula da ɓangaren.
A cewar mataimakin gwamnan, ma’aikatan sun haɗa da likitoci, ma’aikatan jinya,anguwan zoma da na fanin gwaje gwaje da masana haɗe haɗen magunguna .
Alhaji Farouk Joɓe ya ce nan bada jimawa ba gwamnati na shirin ƙara
ɗaukan ma’aikatan a karo na uku.
Kan karancin likitoci a jihar kuma mataimakin gwamnan ya bayyana cewa tuni gwamnatin jihar ta tura ɗalibai 41 ƙasar Misra don su koyo karatun aikin likita inda gwamnatin ta kashe masu kuɗi fiye da Naira biliyan biyu.
Adadin kuɗin sun haɗa da biyan kudin makaranta, wurin kwana, safarar su zuwa da dawowa da ɗawainiyar yau da kullum har zuwa lokacin da zasu kammala karatu.
Haka kuma gwamnatin Dikko Raɗɗa ta ƙara albashin likitoci sabbin ɗauka da kuɗin alawus na masu neman ƙwarewa,domin basu ƙwarin gwiwa.
Duk dai a ƙoƙarin ta na inganta harkar lafiya, Malam Farouk Joɓe ya sanar da cewa gwamnati ta soma bada horo kan ƙwarewar aiki a fagen kula da lafiyar mata da iyali a asibitin kula da mata da ƙananan yara a Asibitin Turai Yar’adua.
