Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusif ya ƙara wa’adin aikin Shekaru biyu ga shugaban ma’aikatan gwamnati da wasu manyan sakatarori.
Gwamnan ya sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, inda ya ce ƙarin wa’adin zai fara ne daga ranar 31 ga Disamba 2024.
Sauran manyan ma’aikatan da aka tsawaita wa’adin aikin nasu sun haɗar da wasu manyan sakatarori Umar Muhammad Jalo, Bilkisu Shehu Maimota, Mu’azatu Isa Dutse, Abdulmuminu Musa, da Tijjani Muhammad Sharif da kuma Bashir Idris Ɗiso a matsayin magatakardar ofishin majalisar dokokin jihar.
Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne bisa dogaro ga sashi na 5 (2) da 208 na kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya na 1999, bayan da lokacin ritayar su yayi a Talata 31 ga Disamba, 2024, a ƙarƙashin dokokin hukumar kula da fansho ta Jihar Kano.
Sauran manyan ma’aikatan gwamnatin da aka ƙarawa shekaru biyun su ne; Kwamared Kabiru Ado Minjibir, Kwamared Marwan Mustapha, Kwamared Tajuddeen Bashir Baba da Kwamared Hashim A. Sule da kuma Kwamared Kabiru Inuwa.
Kazalika, akwai waɗanda suka fito daga fannin lafiya, irin su Amina Idris da Ahmad Lawan da Hussaini Nuhu da Salisu H. Nadosun da kuma Larai Ahmadu.
Sanarwar da daraktan wayar da kai na Ofishin shugaban ma’aikata Aliyu Yusuf ya fitar, ta ce an umarci duk waɗanda suka ci gajiyar wannan ƙarin wa’adi da su ci-gaba da tafiyar da ayyukan ofishin da aka tura su kamar yadda dokar ma’aikata ta tanada.
