Mutane 2,425 muka kama bisa zargin aikata laifuka a shekarar 2024 – ‘Yan sandan Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya ce rundunar ta sami nasarar kama waɗanda take zargi da aikata laifuka daban-daban har 2,425 daga ranar 1 ga watan janairu zuwa Disamban 2024.

Dogo Garba na bayyana hakan ne a yayin da yake ƙarin haske kan nasarorin da rundunar ta samu, inda ya ce sun kuma kwato muggan makamai, ƙwayoyi da kuma kayan sata.

Ya ƙara da cewa a farkon shekarar 2024, an yi fama da yunƙurin ‘yan bindiga na shigowa jihar wanda suke da ƙananan hukumomi 17 akan iyakokin jahohin, Kaduna, Katsina, Jigawa da kuma Bauchi, baya ga barazanar faɗan daba da kuma masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a ƙananan hukumomin 8 na ƙwaryar birnin Kano.
Ƙanananhukumomi 19 waɗanda basa cikin birni ko kan iyaka, da aka samu yawan sace-sace da faɗa tsakanin makiyaya da manoma.

Cikin nasarorin da rundunar ta samu sun haɗa da cafke yan fashi da makami 189, masu garkuwa da mutane 34, ɓarayin shanu 10, masu safarar bindigu biyu, ɓarayin motoci 22, dilolin ƙwaya 58, masu fasa ƙaurin 18, ɓarayin adaidaita sahu 46 da ɓarayin babura 28 dama cafke masu buga takaddun bogi huɗu, ‘yan damfara 27 da kuma yan daba 1987.

Kazalika ya ce, sun tseratar da mutane 40 da aka yi safarar su da kuma kuɓutar da mutane 18 waɗanda aka yi garkuwa da su , sai mutane biyu da aka sace, baya ga ƙwato bindiga kirar AK-47 guda 7, Beretta Pistol ɗaya, Pump Action huɗu, bindigar harbin tsintsaye 7 ƙirar gida da kuma bindigar wasan yara huɗu.

Haka kuma an ƙwato harsasai 1,213, adduna 57, wuƙaƙe 198, motoci 12, babura 44, adaidaita sahu 15, kuɗin jabu naira Bilyan 129 da Milyan 542 da dubu 823 na kuɗaɗen ƙetare da kuma na Nijeriya, sai shanun sata 308, Katin cirar kudi (ATM Card) 65, wayoyin sata 415, zoben azurfa 67, baturan sola 34 da kuma allura 105.

Sannan rundunar ta ƙarƙare da ƙarshe rundunar ta godewa gwamnatin jihar Kano, sauran hukumomin tsaro, ƙungiyoyin al’umma da kuma kafafen yaɗa labarai da wakilan su, a bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen wayar da kan jama’a musamman akan abinda ya shafi tsaro.

By ukarofi