Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A daidai lokacin da mu ke murnar shiga sabuwar shekara ta 2025, Blueprint Manhaja ta yi waiwayen wasu muhimman al’amura da suka fi ɗaukar hankalin ‘yan Nijeriya a 2024, waɗanda suka tayar da ƙura, cece-kuce, sambarka da makamancin haka, musamman na daga matakan gwamnati da sauran ɓangarori:
Shari’ar zaɓen Gwamnan Kano:
A ranar 12 ga watan Janairu 2023 ne, Kotun Koli ta tabbatar wa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP kujerarsa inda ta soke hukunce-hukuncen da kotunan baya masu cike da ruɗani da kuma karo da juna.
Hakan na zuwa ne bayan hukuncin da Kotun ɗaukaka ƙara ta Tarayya ta yanke, inda ta ƙwace kujerar Abba, amma takardar hukuncin da ta fitar kuma ta tabbatar masa da kujerar.
Kotun ƙoli ta sanar da hukuncin ne bayan ta yi watsi da ƙararrakin da APC ta shigar na zargin aringizon ƙuri’u da kuma iƙirarin cewa Abba ba halastaccen ɗan NNPP ba ne, da ke da hurumin shiga zaɓe.
Alƙalin da ya karanta hukuncin, Mai Shari’a Inayng Okoro, ya sanar cewa kotun ɗaukaka ƙara ta yi kuskure wajen soke ƙuri’un Abba da ake taƙaddama a kan sahihancinsu, hasali ma, babu hujjar da ta tabbatar cewa ba su ne aka jefa a zaben ba. Sannan batun zaman Abba ɗan takarar gwamna a NNPP abu ne na cikin gidan jam’iyyar, don haka wanda ba dan jam’iyyar ba shi da hurumin tsoma baki a ciki.
Mai Shari’a Okoro ya shawarci alkalai da su rika yin duba na tsanaki kan kararrakin da aka kawo gabansu kafin su yanke hukunci.
Shari’ar dai ta samu asali ne da karar da APC ta shigar gaban Kotun Sauraron ƙararrakin Zaɓen Gwamnan Jihar Kano tana ƙalubalantar nasarar Gwamnan Abba, inda take neman a ayyana Gawuna ba Abba ba. Bayan nasarar APC a shari’ar farko ne Abba da NNPP suka garzaya zuwa Kotun ƙoli domin ƙalubalantar hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara ta Tarayya.
Sau biyu gwamnan Kanon yana daukaka kara kan shari’ar, da nufin kare kujerarsa, da kuma rashin gamsuwa da hukuncin Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnan Jihar Kano da kuma Kotun ɗaukaka ƙara ta Tarayya da suka kwace kujerarsa.
Yarjejeniyar Samoa:
Duk da cewa a watan Nuwamban 2023 ne Nijeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar ta Samoa ƙarƙashin ƙungiyar ‘Organisation of African, Caribbean and Pacific States’ (OACPS), labarin ya ɓulla ga jama’a ne a shekarar 2024.
Tun bayan ɓullar labarin sanya hannu kan yarjejeniyar, ‘yan Nijeriya suka ɓarke da zazzafar muhawara keta ce-ce-ku-ce game da yarjejeniyar musamman kan wasu batutuwan da ta ƙunsa.
Babban abin da ya janyo cece-ku-ce kan batun sanya hannu kan yarjejeniyar shi ne batun ‘yancin ɗan Adam.
Sashe na 11 na dokar wanda ya shafi rungumar kowa domin zama al’umma ɗaya ya ce “ƙasashen OACP za su ɗauki matakan ganowa da magance matsalar tsangwama bisa kowane irin dalili, kamar bambancin launin fata, da jinsi, da harshe, da addini, da ra’ayin siyasa, da haihuwa, da nakasa, da shekarun haihuwa da kuma jinsin mutum.”
Wannan sashe ne ya haifar da tayar da haƙarƙari, inda wasu ƙungiyoyi suka yi tir da dokar duk kuwa da cewa gwamnatin Nijeriya ta yi bayani kan cewa babu batun auren jinsi a dokar.
Mafi ƙarancin albashi
A ranar Alhamis, 19 ga watan Yunin 2024 ne Shugaban Nijeriya Bola Tinubu da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar suka sanar da matsaya kan naira 70,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikatan ƙasar.
Hakan na nufin an nunka tsohon albashi mafi ƙanƙanta na 30,000 fiye da sau biyu.
ƙarin albashin mafi ƙanƙanta ya zo ne bayan kai ruwa rana da aka yi tsakanin ɓangaren gwamnati da na ‘yan ƙadago game da buƙatar ƙarin albashin domin yin daidai da halin da ƙasar ke ciki.
Sai dai sabon albashin mafi ƙanƙanta ya gaza wanda ƙungiyoyin ƙwadagon suka gabatar na naira 250,000.
A lokacin da yake jawabi ga manema labaru, Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC, Joe Ajaero ya ce “a halin da ake cikin yanzu an tsaya ne kan naira 70,000, amma wani abin jin daɗi shi ne ba za mu tsaya har sai nan da shekara biyar kafin a sake duba albashin mafi ƙanƙanta ba.
Shari’ar masarautun Kano
Idan akwai wani abin da za a manta ya faru a shekara 2024, to tabbas banda dambarwar Masarautun Kano, domin kuwa, al’amari ne da ya ɗauki hankali mutane a ciki da wajen Nijeriya, kuma har yanzu ana ci gaba da kai ruwa rana ba tsakanin gwamnati da bangarorin da ke ikirarin halascin sarautar kowannensu.
A watan Yuni ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar dokar masarautu, wadda ta rushe sabbin masauratu biyar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro, ta kuma bai wa Gwamnan damar dawo da Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarki na 16.
Bayan sanya hannun a kan dokar sabbin masarautun suka dauki dangana, banda Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda a lokacin yake kasar waje, amma ya dawo Kanoya tare a karamar fadar Nassarawa.
A yayin da lamarin ke kotu, ɓangaren Sarki Aminu sun shigar da ƙarar neman soke naɗin Sarki, a yayin da gwamantin ke neman tabbatar da shi da samun umarnin hana Aminu bayyana kansa a matsayin basaraken Kano.
Lamarin dai ya haifar da ruɗani, inda gwamnatin jihar ke zargin ya samu goyon baya daga gwamnatin tarayya da ke neman mayar da shi kan kujera da ƙarfin tsiya, inda aka jibge masa jami’an tsaro da ke gadin fadar Nassarawa.
Dambaruwar masarautar Kano ta kai ga kowane tsagi ya shigar da ƙara a kotu, wanda hakan ya sa kotu yanke hukunci mabambanta. Har yanzu haka dai ana ci gaba da wannan shari’ar.
Lamarin dai ya kai yin musayar kalamai tsakanin tsagin gwamnatin APC da NNPP a Kano. Sai dai masu ruwa da tsaki da shugabanni sun yi kira da yi sulhu domin samun zaman lafiya a jihar.
Taƙaddamar Dangote da NNPC:
A ƙarshen shekarar 2023 ne matatar ɗangote ta tabbatar da cewa ta fara karɓar ɗanyen man fetur wanda za ta fara tacewa domin samar da man fetur da sauran abubuwan amfani.
Matatar wadda aka kashe dala biliyan 20 wajen gina ta, ita ce mafi girma a Afirka, wadda za ta iya tace gangar man fetur 650,000 a rana, kuma an yi fatan cewa za ta kawo ƙarshen matsalolin da Nijeriya da daɗe tana fuskanta a ɓangaren man fetur.
Sai dai ya zuwa farkon 2024, matatar ta ɗangote ta riƙa samun saɓani da kamfanin mai na Nijeriya NNPCL, inda kamfanin ya fara cewa sinadarin sulfur da ke cikin man matatar ya zarta adadin da ake buƙata.
Haka nan kuma shugaban hukumar kula da harkar man fetur ta Nijeriya (NMDPRA) Farouk Ahmed, ya faɗa wa taron manema labarai cewa “man fetur ɗin matatar ɗangote bai kai ingancin wanda ake shigowa da shi ba”.
Haka nan NNPCL ya zargi ɗangote da ƙoƙarin “yin babakere a harkar man fetur”.
Saɓanin ya yi zafin da har Aliko ɗangote ya bayyana cewa a shirye yake ya sayar wa NNPCL da matatar ta biliyoyin daloli.
A martanin da ya mayar, shugaban rukunin kamfanonin ɗangote, Aliko Dangote ya ce:
“NNPCL na iya sayen matatar don tafiyar da ita yadda yake so. Sun bayyana ni a matsayin mai babakere a harkar kasuwanci. Wannan ba gaskiya ba ne kuma bai dace ba, amma babu laifi. Idan za su saya, aƙalla za su yi maganin wanda suka kira mai babakere.”
Shari’ar Emefiele
A 2024 EFCC ta ci gaba da gurfanar da tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, inda a karon farko Babbar Kotun Tarayya ta ba shi fita daga yankin Abuja bayan buƙatar hakan da lauyansa, Mathew Bukka, SAN ya gabatar, yana neman ta sauya sharuddan belinsa da ta bayar.
A ranar 23 ga Nuwamba, 2023, Mai Shari’a Hamza Mu’azu ya ba da belin Emefiele, wanda Hukumar yaƙi da masu karya tattalin arzikin ƙasa (EFCC) ta gurfanar kan zargin badaƙalar biliyoyin kuɗaɗe a lokacin shugabancinsa a CBN.
A lokacin, Mai Shari’a Hamza Mu’azu ya shardanta wa Emefiele ajiye kuɗi Naira miliyan 300 da kuma kawo mutum biyu waɗanda kowannensu ya mallaki gida a unguwar Maitama a Abuja su tsaya masa.
Haka kuma alkalin ya shardanta wa tsohon gwamnan na CBN cewa ba zai fita daga Abuja zuwa wani waje ba. Amma a zaman na ƙarshe, lauyansa, Matthew Bukkak, ya buƙaci a janye sharadrin hana shi fita daga Abuja, yana mai cewa a matsayin Emefiele na babban mutum, ba zai tsere ba idan aka yi masa sassaucin fita daga Abuja, hasali ma takardunsa na tafiye-tafiye suna hannun kotu.
Har yanzu dai Emefiele na hannun hukumomi a tsare, inda ake ci gaba da shari’arsa.
’Yancin ƙananan hukumomi:
An shafe shekaru, ƙananan hukumomi na ƙarƙashin ikon gwamnonin jihohi ta fuskantar tafiyar da kuɗinsu – ta hanyar wani asusu da ake kira na haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jiha da ƙananan hukumomi da kuma wurin zaɓen sabbin shugabanni.
Sai dai a wani hukunci da ta yanke a farkon watan Yuli, Kotun ƙolin Nijeriya ta ce iko da kuɗaɗen ƙananan hukumomi da gwamnoni ke yi ya saɓa wa kundin tsarin mulki.
Alƙalin da ya jagoranci hukuncin Emmanuel Agim ya ce ƙananan hukumomi 774 na Nijeriya su ne ke da haƙƙin tafiyar da kuɗaɗensu da suke samu daga kason tarayya.
Kotun ƙolin ta ƙara fayyace ƙarfin ƙananan hukumomi inda a hukuncin ta ce tana cikin matakan gwamnati; Tarayya da jiha da kuma ƙaramar hukuma.
Kotun ta kuma ce gwamnatin jiha ba ta da ikon naɗawa da kuma tuɓe shugabannin riƙo na ƙananan hukumomi, dole sai ta hanyar zaɓe.
Ana ganin cewa wannan mataki ya sanya jihohi da dama sun garzaya domin gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi.
Sai dai ya zuwa ƙarshen shekarar ta 2024 an ci gaba da kokawa kan cewa har yanzu akwai jihohi da dama da ba su fara amfani da hukuncin kotun ba.
ƙudurin haraji:
A farkon watan Oktoban 2024 ne Bola Tinubu ya aika da wasu ƙudurorin huɗu gaban majalisar dokokin ƙasar domin neman amincewarta.
Jim kaɗan bayan haka ne kuma gwamnoni – na APC da na adawa – da ma wasu ‘yan ƙasa da dama suka fara nuna adawa.
Yayin wani taro da ƙungiyar gwamnonin arewacin ƙasar ta yi a Kaduna a ƙarshen watan Oktoba, sun ce sabon ƙudirin ya saɓa wa muradun jihohinsu, kuma suka yi kira ga ‘yan majalisar yankin su yi watsi da shi a zauren majalisar dokokin ƙasar.
“Abin da ya sa ba mu yarda ba shi ne, ana karɓar harajin VAT ne a hedikwatar kamfanonin maimakon inda sauran rassan kamfanonin ke gudanar da ayyukansu ko sayar da kayayyakinsu,” in ji shugaban ƙungiyar Gwamnan Gombe Muhammad Inuwa Yahaya – wanda ɗan APC ne.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum na daga cikin waɗanda suka fito ƙarara suka yi adawa da dokar.
Haka nan an tafka zazzafar muhawara kan dokar a majalisar dattijan ƙasar ta Nijeriya.
Sai dai babbar muryar da aka fi ji wajen adawa da wannan ƙudiri ita ce ta Sanata Ali Ndume mai wakiltar mazaɓar Borno ta Kudu a majalisar dattawa.
Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna yadda gogaggen sanatan na jam’iyyar APC ya dinga musayar kalamai da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin (wanda ya jagoranci zaman a ranar) kan ƙudirin.
Sace ɗaliban Kuriga:
A farkon watan Maris ne aka tashi da labarin sace ɗaliban makaranta 280 a garin Kuriga da ke ƙaramar Hukumar Chikun a jihar Kaduna.
Sa dai a lokacin da hukumomi suka sanar da kuɓutar da yaran, sun ce sun yi nasarar ƙwato mutum 137 saɓanin adadin da mahukuntan makarantar suka sanar a lokacin da lamarin ya faru.
Sannan ɗaya daga cikin malaman makarantar da aka sace su tare da ɗaliban, ya rasu a hannun masu garkuwar.
ɗaliban sun shafe kwana 17 a hannun masu garkuwa kafin hukumomi su kuɓutar da su ‘yan kwanaki kafin cikar wa’adin biyan kuɗin fansa da masu garkuwar suka bayar.
Satar ɗaliban a lokacin ya sake tunowa da mutane batun ‘yan matan Chibok da ƙungiyar Boko Haram ta sace a makarantarsu da ke jihar Borno cikin shekarar 2014.
Sace Sarkin Gobir da kisan sa
Sace Marigayi Sarkin Gobir na Gatawa Isa Bawa na ɗaya daga cikin sace-sacen da aka yi cikin 2024 da ya jefa al’umma cikin jimami.
Kwana uku bayan sace shi, ‘yanbindigar sun fitar da wani bidiyo inda aka ga marigayin yana neman da a kai masa ɗauki domin kuɓutar da shi.
Sai dai bayan kwanaki 25 da kasancewa a hannun masu garkuwar ne kuma aka samu labarin mutuwarsa.
Duk da cewa ‘yanbindiga sun kwashe shekaru suna kashe-kashe a yankin na arewacin Nijeriya, amma ba kasafai ake samun irin haka ba.
Mutuwar Sarkin ta ƙara fito da matsalar taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya.
Sace mahaifiyar mawaƙi Rarara:
A cikin watan Yuni ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da Hajiya Hauwa’u Adamu, mahaifiyar fitaccen mawaƙin Hausa, Dauda Kahutu Rarara.
Katsina na daga cikin jihohin arewacin Nijeriya da ke fuskantar matsalar tsaro, inda ‘yanbindiga ke kashewa tare da yin garkuwa da mutane.
‘Yan sanda, a lokacin sun ce sun kama mutum biyu bisa zargin hannu a sace mahaifiyar ta Rarara.
Sai dai bayan shafe mako uku a hannun ‘yanbindigar ne Hajiya Hauwa’u ta samu kuɓuta.
Shari’ar ’yan zanga-zangar yunwa:
Gwamantin Nijeriya ta gurfanar da ƙananan yara a kotu kan zargin yunƙurin kifar da gwamnati a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da yunwa da aka yi a ƙasar a watan Agusta.
A lokacin gurfanar da yaran waɗanda aka tsare na tsawon watanni a gidan yarin Kuje ne wasu daga cikinsu suka sume, babu shiri Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da zaman, kafin daga bisani Mai Shari’a Obiora Egwuatu ya ci gaba da zaman bayan an fitar da su domin duba lafiyarsu.
Daga baya alƙalin ya bayar da su beli a kan Naira miliyan 10 kowannensu tare da umarnin tsare su a Gidajen Yarin Kuje har sai an cika sharuɗan belin da suka haɗa da kawo wani babban ma’aikacin Gwamnatin Tarayya da ya mallaki lasisin tuƙi da kuma lambar shaidar ɗan ƙasa ya tsaya musu. Haka kuma za su kawo takardar kyakkyawar shaida daga iyayensu ko kamu ’yan uwansu.
Wannan hukunci ya bar baya da ƙura, inda dubban mutane suka fara sukar gwamnatin Nijeriya, inda a ƙarshe Shugaba Tinubu bayar da umarnin sakin su, gwamnatin tarayya ta miƙa yaran ga gwamnnonin jihohinsu.
Shari’ar Yahaya Bello:
Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, bayan shafe watanni yana wasan ɓuya da hukumar da ke zargin sa da karkatar da dukiyar jama’a kimanin Naira biliyan 1100 a lokacin da yake gwamna. A ƙarshe ya miƙa kansa ga hukumar ta kai shi kotu, inda ta tsare shi a Gidan Yarin Kuje.
Mai shari’a Maryanne Aninih, ta umarci EFCC ta tsare Bello a hannunta, tare da sanya ranar 10 ga watan Disamba domin yanke hukunci kan buƙatar bayar da belinsa.
Lauyoyi daga ɓangarorin EFCC da Bello sun yi muhawara kan buƙatar bayar da belinsa. Lauyan Bello, Joseph Daudu (SAN), ya roƙi kotun ta bayar da belinsa, inda ya ce laifukan da ake tuhumar tsohon gwamnan na cikin waɗanda za a bayar da beli.
Sai dai lauya mai gabatar da ƙara, Kemi Pinheiro (SAN), ya ƙalubalanci buƙatar belin. Bello, tare da wasu tsoffin jami’an gwamnatin Kogi, Abdulsalami Hudu da Umar Oricha, an zarge su da haɗa kai wajen amfani da kuɗaɗen gwamnati don sayen kadarori a Abuja da Dubai, na kimanin Naira biliyan 110.4.
Kafin fara zaman kotun, an tsaurara tsaro a wajen kotun, inda jami’an sojoji, DSS, EFCC, da ‘yan sanda suka yi dafifi. Bello ya shiga ɗakin kotun sanye da farar babbar riga da hula mai launin shuɗi mai haske.
Sai dai hakarsa ta cimma ruwa a ranar Juma’a 20 ga watan Disamaban 2024, inda kotun ta bayar da belinsa kan wasu sharuɗɗa.
