
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya ziyarci Kurkukun Kaduna don ganin tsohon shugaban ma’aikatan gidan gwamnatinsa, Bashir Sa’idu da aka tsare.
A ranar Litinin ne aka kama shi tare da kai shi wata kotun shari’a dake Rigassa wadda ta umarci a tsare shi a gidan yarin bisa zargin sa da hannu a badaƙalar wasu kuɗaɗe da ma wasu tuhume-tuhume.
Rahotanni sun ce El-Rufa’i ya je gidan yarin ne tare da wasu tsofaffin kwamishinoninsa da suka haɗa da; Kwamishinan Ilimi, Jafaru Sani; Kwamishinar Ci-gaban Al’umma, Hafsat Baba; da kuma Ibrahim Hussaini wanda shi ne tsohon Kwamishinan kula da muhalli.
Yayin da ƴan jarida suka yi ƙoƙarin ji daga bakin El-Rufa’i, bai saurare su ba inda ya kauce wa yin tsokaci.
