Gwamnatin Tarayya ta ceto matar da aka yi safarar ta daga Iraƙi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Juma’a, 3 ga watan Junairu, 2025 ne wata ƴar Nijeriya mai suna, Eniola Isaac za ta dawo ƙasar bayan wakilan Nijeriya a Jordan sun shiga tsakani da ƙasar Iraƙi.

Hakan na zuwa ne bayan wani rahoto da ke zargin cewa an yaudari matar ne mai shekaru 28 da cewa za a kai ta Iraƙi don samun rayuwa mai daɗi.

Bayan ta sha duka da wasu nau’ukan wulaƙanci, sai Eniola ta koka ga hukumomin Nijeriya don su dawo da ita ƙasarta.

Cikin wani rahoto da NiDCOM ya fitar a ranar Alhamis ta kafar X, ya ce safarar ƴan Nijeriya zuwa Iraƙi bisa yaudara ya zama ruwan dare.

Ana cigaba da gudanar da bincike kan wata mata da aka yi safarar ta zuwa ƙasar da sunan aiki, wadda daga ƙarshe ta rasa ranta.

NiDCOM ta yi gargaɗin cewa a yanzu akwai wakilan da ke yaudarar al’umma da sunan zuwa aiki ƙasar Iraƙi bisa alƙawura na ƙarairayi wanda hakan yake zama haɗari ga rayukansu, inda wasu ke zama bayi yayin da wasu kuma suke faɗa wa harkokin karuwanci.

By Babaji