
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Tsohon ɗan takarar Shugaban ƙasa, ƙarƙashin jam’iyyar PDP Gbenga Olawepo Hashim ya bayyana marigayi Ahmadi Kurfi a matsayin dattijon da ake girmamawa ba a iya Katsina kaɗai ba har ma a Nijeriya baki ɗaya.
Mista Gbenga ya faɗi haka ne a Katsina a lokacin da ya je ta’aziyya ga iyalan Marigayi Alhaji Ahmadi kurfi a gidansa da ke cikin garin Katsina.
Ya ce ya san marigayi Ahmadi Kurfi mutum ne mai basira, hangen nesa da son zaman lafiya.
“Irin waɗannan halaye na marigayi Ahmadi Kurfi ne aka rasa a Nijeriya”, inji Gbenga.
Ya kuma yi fatan Allah masa rahama ya kuma bai wa iyalansa haƙuri na rashin da sukayi tare da cigaba da yi masa addu’a.
Marigayi Ahmadi kurfi tsohon ɗan kasuwa ne kuma jigo a PDP, haka kuma ya taɓa riƙe muƙamin ɗan kwamitin Amintattu a tsohuwar jam’iyyar Peoples Front ta marigayi Janar Shehu Musa Yar’adua.
A wajen karɓar gaisuwar akwai babban amininsa kuma tsohon sakataren PDP na ƙasa ,Sanata Umar Tsauri da babban ɗan marigayi kuma shugaban jam’iyyar PDP a jihar Katsina Alhaji Nura Ahmadi Kurfi.
