
Daga BELLO A. BABAJI
Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya bayyana gamsuwarsa ga ƙoƙarin Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule musamman a ɓangaren samar da abinci, ya na mai cewa ya cika wa ƴan jihar alƙawarin da ya yi mu su.
Ya ce Gwamna AA Sule ya mayar da jihar tamkar madogara a harkokin noma a Nijeriya.
Shettima ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a, yayin ziyarar aiki na kwana ɗaya da ya kai Lafiya, babban birnin jihar inda ya ƙaddamar da raba tiraktoci da buhunan shinkafa ga al’umma daga ɗaukacin ƙananan hukumomi 13 dake jihar.
An gudanar da taron ne a gidan gwamnatin jihar inda aka kuma raba kayan tallafi ga waɗanda iftila’in ambaliya ya shafe su a shekarar 2024.
Mataimakin Shugaban ƙasar ya ce jihar ta ɗauki matakin ciyar da Nijeriya abinci, ya na mai cewa za su bada duk gudunmawar da ake buƙata don ganin an cimma hakan, wanda zai taimaka wajen magance matsalolin rashin wadataccen abinci a ƙasar.
Ya ƙara da cewa, Gwamantin Tarayya, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, za ta haɗe kai da ta jihar tare da tallafa mata don cimma kyawawan manufofinta.
Kazalika, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta cigaba da tallafa wa marasa galihu waɗanda annoba ta shafe su don sauƙaƙa musu halin rayuwa.
