Nijeriya ta yi nasarar cimma burinta na cike giɓin da take samu wajen haƙo mai wanda ƙungiyar ƙasashe masu albarkatun mai OPEC ta kayyade mata na haƙo ganga miliyan 1.5 a kowace rana.
Wannan shine
karon farko cikin shekaru huɗu da Nijeriya ta sami irin wannan gagarumar nasara tun bayan dawowar matsalar masu fasa bututun mai da gwamtocin baya suka fuskanta.
Wasu alƙaluman binciken Bloomberg sun nuna cewa yawan man da Nijeriya ke haƙowa ya ƙaru da ganga 40,000 zuwa miliyan 1.51 a watan Disambar bara.
A baya dai ƙungiyar OPEC ta ware wa Nijeriya damar haƙo ganga Milyan 1.8 a kowace rana, sai dai ƙungiyar ta rage wannan adadi zuwa milyan 1.5 sakamakon gazawar Nijeriya na cike giɓin da take samu wajen haƙar man ta dalilin matsalolinta na cikin gida, hakan ya janyo wa kasar koma-baya a ɓangaren tattalin arzikin sakamakon raguwar kuɗaɗen shiga da masu zuba jari.
Sai dai jim kaɗan da ɗarewar Shugaba Tinubu karagar mulkin ƙasar, ya lashi takobin dawo da Nijeriya gurbinta ta hanyar magance matsalolin tsaron yankin da ke da arzikin man dama Nijeriya baki ɗaya.
Ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, ya danganta wannan nasarar da ƙoƙarin da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi na ganin an ƙara yawan albarkatun man fetur da suka haɗa da jawo jarin ƙasashen waje da kuma tabbatar da zaman lafiyar al’ummomin da ke zaune a yankunan haƙar mai.
