Abinda ya kamata mu sani akan cutar HMPV

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

A cikin ‘yan kwanakin nan, cutar da ake kira Human Metapneumovirus (HMPV) ta yi tsanani a yankunan Arewa maso gabashin ƙasar Sin, inda ta fi addabar yara. Wannan annoba ta haifar da cunkoson marasa lafiya a asibitoci, abin da ya tuna wa mutane da farkon bayyanar cutar Covid-19. Hukumar kula da cututtuka ta ƙasar ta bayyana cewa adadin masu kamuwa da cutar ya ƙaru sosai a wannan lokaci fiye da na bara. HMPV tana haifar da alamomi makamantan mura, kamar tari, rashin lafiya, zazzabi, da kumburin hanci.

Duk da haka, tana iya haifar da matsaloli masu tsanani kamar ciwon huhu, rashin numfashi, da kuma tari mai ƙarfi.

Masana sun gargaɗi jama’a kan lura da alamomin cutar musamman ga yara da tsofaffi. Farfesa John Tregoning daga Imperial College London ya bayyana cewa cutar tana kama da cutar RSV kuma tana yaɗuwa ta hanyar tari, atishawa, da saukar ruwa daga hanci ko baki. Ya bada shawarar zama a wuraren da ke da iska mai kyau, wanke hannu akai-akai, da rufe baki yayin tari ko atishawa don rage yaɗuwar cutar.

Duk da haka, babu rigakafi ko magani na musamman ga HMPV a halin yanzu; ana magance ta ne ta hanyar rage alamomi da samun hutu.

Farfesa Jaya Dantas daga Curtin University ta yi kira ga mutane su ɗauki matakan kariya, kamar gwajin cutar idan ana zargin kamu, zama a gida, sanya abin rufe fuska a bainar jama’a, da kare masu rauni kamar yara ƙanana da tsofaffi. Ta ƙara da cewa HMPV tana iya zama mai tsanani ga waɗanda ke da ƙarancin garkuwar jiki, tana iya zama ciwon huhu mai tsanani ko pneumonia. Duk da haka, wasu masana sun bayyana cewa ƙaruwar cutar ba abin firgici bane, kuma HMPV tana yaɗuwa cikin mutane tun kimanin shekaru 50 da suka gabata.

A halin yanzu, rahotannin hukumar kula da lafiya ta Sin sun nuna cewa kashi 7.2 cikin 100 na masu zuwa asibiti a arewacin ƙasar suna fama da alamomin mura, wanda ya ƙaru da kashi 12 cikin 100 a makon da ya gabata. Haka zalika, a kudancin ƙasar, kashi 5.7 cikin 100 na masu zuwa asibiti suna fama da cutar, wanda ya ƙaru da kashi 21 cikin 100 daga makon da ya gabata. Wannan ci gaba ya zarce adadin bara a wannan lokaci, sai dai bai kai matakan shekarun 2022 da 2023 ba. A ƙasashen turai ma, musamman Ingila, adadin masu fama da mura ya ninka fiye da na bara, inda aka yi hasashen cewa matsalar za ta ƙara tsanani bayan bukukuwan Kirsimeti da sabuwar Shekara.

By ukarofi