Tinubu ya dawo Abuja daga Ghana

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan kusan makonni uku baya Abuja.
Jirgin Airbus A330 da ya ɗauko Shugaban ƙasar da muƙarrabansa ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe, Abuja, da misalin ƙarfe 10:30 na dare.

Tinubu ya samu tarba daga shugaban ma’aikatansa, Femi Gbajabiamila, mai ba da shawara kan tsaron ƙasa, Nuhu Ribadu, da sauran manyan jami’an tsaro.

Tinubun ya dawo ne daga Accra, Ghana, inda ya halarci rantsar da Shugaba John Mahama a ranar Talata.

A yayin tafiyarsa daga Abuja, shugaban ƙasar ya kuma ziyarci Jihar Enugu. A ranar 18 ga Disamba, 2024, shugaba Tinubu ya bar Abuja zuwa Lagos, inda ya yi bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.

By ukarofi