Gwamnan Dauda ya gana da ministan kiwo, ya ce Zamfara ta shirya wa kiwon zamani

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya tabbatar wa sabuwar Ma’aikatar Ci-gaban Kiwo da aka samar a Nijeriya cewa jiharsa ta na da wadataccen filaye na gudanar da harkokin kiwo.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara ga Ministan Ma’aikatar, Alhaji Idi Maiha a Hedikwatarta dake Abuja.

Wata sanarwa da Kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce gwamnan ya jaddada cewa Zamfara jiha ce mai arziƙin harkar noma da kiwo, saboda haka za ta taimaka matuƙa wajen ayyukan ma’aikatar.

Gwamna Dauda ya bayyana muradin Gwamantinsa tana bada haɗin kai ga samun nasarori a jihar musamman kan harkokin gona.

Ya kuma yi murna ga samar da ma’aikatar, yana mai cewa jiharsa za ta haɗa gwiwa da ita wajen cimma ayyukan ci-gaba.

Ya ƙara da kira ga ministan da ya ziyarci Zamfara domin ganin irin albarkatu da damammakin da take da su ganin yadda ma’aikatar za ta taimaka wajen zamanantar da ɓangaren ta hanyar shirye-shirye.

A watan Yulin 2024 ne Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da ma’aikatar don samar da yanayi mai kyau ga masana’antar kiwo da faɗaɗa damammakin zuba hannun-jari da wadataccen abinci a Nijeriya.

By ukarofi