Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin jihar Katsina ta tallafa wa iyalan waɗanda yan bindiga suka kashi a wasu ƙauyuka da ke ƙaramar hukumar Charanchi.
Kauyukan sun haɗa da Kartaka, Farfaru da Dangaladima da suke gundumar Raɗɗa.
Da yake jawabi bayan ya kammala raba kuɗin mataimaki na musamman kan yaƙi da ta’adanci da kuma kula da yan gudun hijira Alhaji Sa’idu Ibrahim ɗanja Kogunan Jibiya ya jajenta wa iyalan da suka rasa nasu.
Ya ce wannan tallafi ba wai diyya ce ga waɗanda suka rasa rayukansu ba, “Gwamna Raɗɗa ya fito da wannan tsari na tallafawa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da kuma waɗanda suka samu raunuka,” inji Kuogunan Jibiya.
Haka ma jami’an tsaro da suka rasa rayukansu a lokacin yaƙi da yan ta’adda a jihar, a cewarsa.
Ya bayyana cewa Gwamna Dikko Raɗɗa ya kuma umurci sashin ilimi na ƙananan hukumomi da su tabbatar sun ɗauki yaran da suka rasa iyayensu makaranta kyau ta.
Jami’an tsaron da suka rasa rayukansu, kowanne na samun tallafi na Naira miliyan ɗaya, waɗanda suka samu raunuka su kuma Naira dubu ɗari biyar kowanne.
Ibrahim ɗanja ya yaba da dangantaka da ke akwai tsakanin gwamnati da jami’an tsaro da kuma al’ummar jihar wanda ya taimaka wajen samun zaman lafiya a sassan da suka yi ta fama da ta’addanci.
