Daga JOHN D. WADA a Lafiya
A yanzu haka Kwamared Jafar Abdullahi ne ya zama sabon mai magana da yawun babbar Jami’ar Jihar Nasarawa dake garin Keffi hedikwatar ƙaramar hukumar Keffi a jihar.
Kwamared Jafar Abdullahi ya hau kujerar ne ta kakakin babban jami’ar mallakar gwamnatin jihar ta Nasarawa jim kaɗan bayan barin muƙamin da tsohon mai magana da yawun jami’ar Mista Abraham Ekpo ya yi sakamakon naɗin sa shi kuma a matsayin sabon babban sakataren ƙaramar hukumar Karu a jihar kwanakin baya.
Binciken wakilinmu dai ya gano cewa kafin wannan sabon matsayin nasa na mai magana da yawun jami’ar Kwamared Jafar Abdullahi ya kasance mataimakin Mista Abraham Ekpo inda suka ta yi aiki tare da daɗewa ba tare da samun matsala ba har zuwa wannan lokaci da Jafar ya ɗare kan kujerar.
A halin yanzu dai shugabanni daban-daban da ma’aikatan jami’ar baki ɗaya ciki har da malamai da abokai da sauran ‘yan uwan sabon kakakin jami’ar suna cigaba da taya shi murnar damar tare da yi masa fatar alheri, kana suna bayyana cewa tabbas kujerar ya dace da shi idan aka yi la’akari da gagaruman gudumawa da ya daɗe yake bayarwa ƙarƙashin Mista Abraham sa’anan kuma a cewar su mutum ne da ya ƙware sosai musamman a fannin hulɗa da jama’a.
Da yake tattaunawa da wakilinmu a sabon ofishin nasa Kwamared Jafar Abdullahi ya gode wa ‘yan uwa da abokan arziki da sauran ma’aikatan jami’ar baki ɗaya dangane da fatar alheri da suke cigaba da yi masa inda ya kuma yi alƙawarin yin duka mai yiwuwa wajen cigaba daga inda aminin nasa Mista Abraham Ekpo ya tsaya musamman ta yin aiki tuƙuru wajen ɗaukaka sunan jami’ar zuwa mataki na gaba tare da yin kira ga kowa ciki har da ‘yan jarida su cigaba da ba shi cikakken goyon baya don a cigaba da cimma nasarorin tare.
