‘Yan bindiga sun sanya wa mutanen ƙauyukan Zamfara harajin kusan miliyan 200

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rahotanni daga garuruwan ƙaramar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara na cewa ‘yan bindiga sun ɗorawa jama’a harajin da ya kai naira miliyan 172 baya ga neman ba su buhunan abinci da makanatan su.

Haka ma a ƙaramar hukumar Bukkuyum duk dai a jihar ta Zamfara an samu rahoton cewa wasu gungun ‘yan bindigar sun yi garkuwa da fiye da mutum 40 waɗanda galibinsu mata ne da yara ƙanana.

Rahotannin na cewa ɓan bindigar ƙarƙashin jagorancin shugabansu ɗan-Isuhu, sun wajabtawa al’ummar yankunan su ba su tarin buhunan waken suya da sauran kayan abinci.

Rahoton wanda wani mai bincike kan sha’anin tsaro a tafkin Chadi ya Zagazola Makama ya rawaito, ya ce ‘yan bindigar sun ɗora musu ɗimbin harajin wuce kima da suka raba a garuruwan Gijinzama masu naira miliyan N8.5 million sai Dakolo mai 5 tare da buhunan waken suya 20 da ƙauyen Gunja da suka ɗorawa mazaunansa harajin miliyan 7 da ƙauyen Kane mai 5 da Kurar Mota da aka tilastawa samo miliyan 6 da za su fansar kansu da sauran garuruwa.

Haraji mafi yawa shi ne wanda aka ɗorawa al’ummar Kunchin Kalgo na naira miliyan 20 yayin da Sungawa da Rakyabu za su biya naira miliyan 15 kowanensu.

Kazalika, duka dai a jihar ta Zamfara, wasu bayanai cewa ƙarin wasu gungun ‘yan bindiga sun afkawa ƙauyen Ganau da ke ƙaramar hukumar Bukuyyum inda suka ƙone gidaje da kuma sace mutane kusan 40 da suka haɗa da mata da yara ƙanana. Wannan lamari dai ya tilasta ɗaruruwan mutane da suka haɗa da mata da yara ƙanana da ake jan hannuwansu na tafiya a kasa tserewa suna barin gidajensu.

Duk ƙoƙarin da Manhaja ta yi na jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar haƙanmu bai cimma ruwa ba, amma kakakin gwamnan jihar Malam Sulaiman Bala Idris, ya ce zafafa hare-haren da ‘yan bindigar suka yi na nuna irin yadda suka rasa mafita ne sakamakon gana masu azaba da jami’an tsaro ke yi, don haka a cewarsa, idan ganga ta fiye zaƙi lokacin fashewarta ne ya yi.

Wannan dai na zuwa ne dai dai lokacin da hare-haren ‘yan bindiga ke ƙara kunno kai a sassan jihar tun bayan da shahararren dan bindigar nan Bello Turji ya bayar da sanarwar far ma garuruwa da yawa a jahohin Sokoto da Zamfara da sauran makwabta muddin ba a sako ɓan uwansa ba, yayin da a hannu ɗaya kuma gwamnatin Nijeriya da ta Zamfarar ke bayyana cewa suna cin galaba akan ‘yan fashin daji.

By ukarofi