Abinda ya sa na fito neman shugabancin ƙungiyar kasuwar waya na titin Bairut – Isah Garba

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Hon. Isah Garba Dan’aljannah tsohon sakataren kasuwar waya na titin Bairut, kuma mataimakin shugaban ƙungiyar masu waya da dangoginta ta Nijeriya AMPAT da sama da shekaru 20 yana kasuwar ya kuma riƙe muƙamai da dama a cikin ta kama daga jami’in hulɗa da jama’a da mataimakin sakatare da sakataren hukumar zaɓe wanda ya bada gudunmuwa a cikin kasuwar wajen kawo cigaba da zaman lafiya.

Ya amsa kiran da ɓan kasuwar waya na titin Bairut suka yi masa na fitowa neman takarar  shugabancin ƙungiyar da ya ke zantawa da ɓan jarida kan wannan kira da aka yi masa Hon. Isah Garba ya ce ba sabon abu ba ne, idan an yi kiran sa ya zo ya nemi shugabancin ƙungiyar kasuwar, idan aka yi la’akari da irin mutane da ya gina da taimakawa, ƙanana suka miƙe waɗanda ba su da sana’a suka samu wajen sana’a da kasuwanci, don haka idan aka shuka alkhairi shi ake girba idan akasin haka aka shuka shi zaka gani don haka wannan kira da aka yi masa ya fito yana neman wannan shugabanci na kasuwar.

Ya yi nuni da  cewa a yanzu kasuwar tana fuskantar ƙalubale da suka soma zuwa musu, da babu su a baya shekaru 18 da suka gabata, cikin manyan ƙalubalen akwai samun matasa da suke shigowa kasuwar suke nema su gurɓata musu tsohon tarihi da suke da shi na zaman lafiya da mutuntaka, sanin da aka yi mata da kasuwanci cikin aminci, amma a waɗannan shekaru uku sun soma ganin canji sakamakon matasa da suke zuwa kasuwar daga wasu wurare ba tare da an yi musu rijista ba, suna kasuwanci wanda suka soma haddasa musu rashin amana a cikin kasuwar da ake yawan samun matsaloli hakan na barazana ga cigaban kasuwar.

ɗan’aljannah ya ce dole a ƙalla wannan abin ya zama an mayar da kasuwar kan tsari da take na asali duk wanda ya zo sai sun san daga ina yake, me ya kawo shi kasuwa, me zai yi  su waye abokan mu’amalar sa, domin su cigaba da riƙe kambun su na kasuwa mafi tsafta a ƙasar nan akan abinda ya shafi hada-hada na harkar waya cikin aminci da gaskiya.

Game da rashin samun babban dila na kamfanin waya a Kano ya yi nuni da cewa duk da mutane suna ƙorafi da hakan, amma nuna sha’awar ka ga abu shi zai sa kamfani ya yi maka dila  ba kamfanin da zai ɗauki dila ya baka ka yi sai ka nema, kuma yin dila yana da kuɗi da yawa, mutanen su suna gani ba za su iya cire waɗannan kuɗi su je su ajiye a  kamfani domin a basu dila ba.

Ya ce domin ƙarƙashin neman dila idan kana so ka zama sai ka ajiye  dala miliyan 1.5. kuɗi ne da ya haura Naira biliyan ɗaya da rabi wannan zaka ajiye ne a matsayin “standing order” na kamfani  wanda shi zai baka damar a fara tantance ka a matsayin dila. Abu na biyu shine tsari na oda duk  wata za ka yi oda sau uku wacce ta kai ta Biliyan Uku kuɗi ne da ake buƙatar sama da  biliyan biyar kafin a ce ka samu dila na waya, mutanen mu wajen cika wannan ƙa’idojin ya kan zame musu me wahala.

Ya ce su sauran abokan zaman mu na Kudu sukan yi amfani da bankunan kasuwanci su karɓi kuɗaɗe a hannunsu su je su saka su a wannan yanayin a cigaba da kasuwanci, wanda mu kuma duba da al’ada da addini ta kan yi tasiri wajen mutane suna ganin bai kamata su karɓi kuɗin ruwa ba, su je su saka shi a cikin irin waɗannan abubuwa, ya na daga cikin abinda ke jawowa ake ganin yan Kano babu dila, amma magana ne na ƙa’ida ko a yanzu in akwai wanda ya cika wannan ƙa’idar yake so kuma a bashi dila, suna da kyakkyawan alaƙa da kamfanonin gaba ɗaya a matsayinsa na mataimakin sakatare na ƙasa na yan waya. Sun yi zama ba ɗaya ba biyu ba, amma ba a sami wanda ya cika wannan ƙa’ida ba, matsalar bana Kano ba ne ko yanzu aka samu wanda ya cika ƙa’ida ƙasa da wata biyu zai zama dila.

Isah Garba ya ce ɗaya daga ƙalubalen shine gwamnatocin Arewacin Nijeriya na da sakaci akan waɗannan abubuwa, Gwamnati bata taimakon yan kasuwa yanda yakamata  abinda ya shafi kasuwanci su kudu akwai ɗauki da suke samu daga gwamnatocin su na jihohi da ƙungiyoyi, amma  sama da shekaru 20 da ya yi a kasuwar titin Bairut  a gwamnatoci da akayi daban-daban ba wanda ya warewa ɓan waya ya ba su tallafin ko da na  N100,00.

Abu ne da ya kamata a zo da tsari ko da ƙananan bankuna ne da za su bai wa ɓan kasuwa jari mara ruwa hakan zai taimaka ƙananan ɓan kasuwa suyi ƙarfi ko a samu wani yanayi da Gwamnati za tayi haɗin gwiwa da yan kasuwa ta tallafa musu su je su sami dila wannan har zuwa yanzu babu.

Hon. Isah Garba Dan’aljannah ya ce amma ba su sani ba wannan Gwamnati ta jihar Kano ta  Injiniya Abba Kabir Yusuf idan an yi zaɓe na ƙungiya ta su ta kasuwar titin Bairut ya yi nasara  za su rubuta koke akan wannan,domin su ga ko akwai abinda za a samu Gwamnati ta shigo ciki ta ga yadda za ta taimaka a samu dila na waya a Arewacin ƙasar nan.

Hon. Isah Garba ya ce shi wannan takara da ya amsa ya fito duk wani abu da zai yi na yaƙin neman zaɓe a shekaru 20 da ya shafe a kasuwar yana bada gudunmuwa ba ya buƙatar ya ce ga abinda zai yi a gaba duk abinda za su yi idan na alkhairi ne al’umma sun gani in akasin haka nema sun sani, sai dai kiran sa ga al’umma shine ka da su kuskura su damƙa amanar dukiyar su da kasuwanci su a hannun mutanen da ba su ma san menene kasuwancin ba, kuma ba su  san ma ya  ake mu’amala a shugabanci ba, wanda yake kamar makaranta ce sai ka koya daga matakin koyo matakin iyawa zuwa na kwarewa ba zai yiwu ka faɗo daga sama baka san ina aka taso ba ina za a  ba, ka zo ka ce ka fito takarar shugabancin al’umma a al’ummar da baka taɓa zama a cikinta ka fahimci ya ya al’amuranta yake ba sannan a yi tsammanin za a samu wani abu na ci gaba.

Shawararsa duk wanda za a zaba a tabbatar da su zaɓi wanda yake da kyakkyawan shaida na mutuntaka da ya iya mu’amala da kowa da kwatanta gaskiya da adalci don a samu cigaba.

By ukarofi